Man United: Dan kwallon Brazil, Telles ya kamu da cutar korona

Alex Telles

Dan wasan Manchester United, mai tsaron baya, Alex Telles ya kamu da cutar korona.

Telles, wanda ya koma United da taka leda daga Porto a farkon watannan, bai buga karawar da kungiyar ta doke RB Leipzig 5-0 a Gasar Champions League ranar Laraba ba.

Kungiyar ta Old Trafford ta sanar a kafarta ta sada zumunta ta Twitter: ''Muna mai fatan samun sauki ya koma buga kwallo tare da 'yan wasa.''

Mai shekara 27 ya killace kansa zuwa kwana 10, daga nan a sake gwada shi kafin ya ci gaba da taka leda.

Kocin United, Ole Gunnar Solskjær ya sayo Telles kan fam miliyan 13.6 da karin Yuro miliyan biyu kudin tsarabe-tsarabe.

Dan kwallon tawagar Brazil ya taka rawar gani a wasan da United ta doke Paris St Germain 2-1 a Gasar Champions League a Faransa a makon jiya.

Sai dai kuma bai buga Gasar Premier League da Manchester United da Chelsea suka tashi 0-0 a Old Trafford.