French Cup: Cutar korana ta sa an dage wasannin gasar zuwa Disamba

French Cup

An dakatar da Gasar kwallon kafa ta French Cup ta maza da ta mata zuwa 1 ga watan Disamba, bayan da ake samun karuwar masu kamuwa da cutar korona da wadanda ke mutuwa a kasar.

Haka kuma hukumar kwallon kafa ta Faransa ta dakatar da Gasar tamaula ta 'yan dagaji nan take.

Firai Minista, Emmanuel Macron ya sanar da dokar zaman gida karo na biyu a fadin kasar har zuwa karshen watan Nuwamba.

Ministan wasanni, Roxana Maracineanu ya ce za a ci gaba da buga manyan Gasar tamaula ta Faransa ba 'yan kallo.

Daga ranar Juma'a za a bar mutane su bar gida ne ga masu aiki na musamman ko jami'an lafiya.

An samu karin masu mutuwa a Faransa da yawa kuma a karon farko, sakamakon cutar korona tun bayan watan Afirilu.

Ranar Laraba mutum 36,437 suka kamu da annobar, yayin da aka tabbatar da mutuwar 244.

Tawagar Faransa za ta kara da ta Ireland a Gasar kwallon zari ruga ranar Asabar a birnin Paris da Gasar kwallon tennis ta kwararru da za a fara ranar Litinin, dukkansu za a yi ba 'yan kallo.

A cikin watan Afirilun bara aka karkare Gasar Ligue 1 ba tare da an kammala ta ba, aka bai wa Paris St Germain kofi a zangon farko da cutar ta bulla cikin watan Maris.

Haka kuma za a hana masu kallon tamaula shiga sitadiya a Jamus, a shirin da kasar ke yi na hana yada cutar korona, bayan da mutane ke kara kamuwa da annobar.