Manchester United: Filinta zai dauki 'yan kallo 23,500 don gudun yada cutar korona

Old Trafford

Manchester United ta gyara wuraren zaman 'yan kallo a Old Trafford da zai dauki mutum 23,00 da tsarin tazara don hana yada cutar korona.

United din ta ce tana mamaki kan yadda gwamnatin Ingila ta hana 'yan kwallo shiga sitadiya domin marawa kungiyoyinsu baya.

Tun farko gwamnatin ta amince 'yan kallo za su fara shiga sitadiya a hankali tun daga farkon watan Oktoba, daga baya ta yi amai ta lashe, saboda samun masu kara kamuwa da cutar korona.

Collette Roche, mai kula da gudanarwa a United ta ce ''Mun karbi bayanan da gwamnati ta gindaya don hana yada amnnobar, na tabbatar za mu iya samar da tsarin da 'yan kallo za su kalli wasa ba tare da wani hatsari ba a filinmu.

A watan jiya Firai minista, Boris Johnson ya ce za a fitar da sabbin matakan kariyar hana yada annobar da za a yi amfani da su wata shida nan gaba.

Rashin shiga filayen ya shafi tattalin arzikin wasanni da kungiyoyi da dama har da United wacce ta yi hasarar kudin shida fam miliyan 70 da ta sa ran samu zuwa 30 ga watan Yunin 2020.

Filin wasa na Old Trafford na daukar 'yan kallo 76,000, kuma shi ne kan gaba wajen daukar mutane da yawa kuma na 11 a nahiyar Turai

A cikin watan Maris aka dakatar da wasanni a Ingila, sakamakon bullar cutar korona, daga baya aka koma buga tamaula amma ba 'yan kallo.