Cristiano Ronaldo: Juve ta ci wasa daya daga hudun da ta yi ba kyaftin din Portugal

  • Mohammed Abdu
  • BBC Hausa

Ranar Laraba, Barcelona ta je Italiya ta doke Juventus da ci 2-0 a wasa na bibiyu na cikin rukuni a Gasar Champions League.

Ronaldo ya soki yadda ake gwajin annobar korona, kuma tun farko Juventus ba ta bayyana shi cikin wadanda za su buga mata Gasar ta Champions League ba ranar Laraba.

Mai shekara 35, ya killace kansa tun lokacin da ya kamu da cutar ranar 13 ga watan Oktoba, an kuma sake gwada shi kafin Labara.

Juventus ba ta ce komai ba kan ko kyaftin din tawagar Portugal na dauke da annobar a lokacin da aka yi masa gwajin.

kungiyar ta yi nasarar doke Dynamo Kyiv 2-0 a wasan farko na cikin rukuni a kakar bana tana da maki uku a wasa biyu.

Barcelona ce ta ɗaya a kan teburi da maki shida, bayan da ta caskara Ferencvaros 5-1 a wasan farko na cikin rukuni a Gasar Champions League ta shekarar nan.

Sama da mako biyu Ronaldo na killace don gudun yada annobar, tuni kuma bai buga wa Juventus wasa hudu ba kenan.

Bai buga wasan da Juventus ta je ta tashi 1-1 da Crotone a gasar Serie A ranar 17 ga watan Oktoba ba.

Bai kuma je Dynamo Kiev a Gasar Champions League da Juventus ta yi nasara da ci 2-0 ba ranar 20 ga watan Oktoba.

Ranar 25 ga watan Oktoba, Juventus ta tashi 1-1 da Verona a gasar Serie A, kuma kyaftin din Portugal bai buga fafatawar ba.

Da karawar da Barcelona ta yi nasara a kan Juventus a birnin Turin da ci 2-0 ranar Laraba a Gasar Champions League.

Ronaldo ya buga wasa shida a bana, guda biyu a tawagar Portugal, sauran a Serie A, ya kuma ci wa kasarsa kwallo biyu, sannan ya zura uku a gasar ta Italiya.

Tun bayan da hukumar da ke kula da gasar Serie A ta bai wa Juventus kwallo uku kan rashin zuwan Napoli buga wasa a Turin, har yanzu kungiyar ba ta yi nasara a karawa uku a gasar ba.

Hakan na nuna karara cewar Juventus ta kasa taka rawar gani sakamakon rashin Cristiano Ronaldo.

Juventus ta hada maki tara a wasa biyar,wadda wannan ce kaka mafi muni tun bayan shekara 10.

A kaka ta biyu da koci Massimiliano Allegri ya ja ragamar kungiyar ta samu maki biyar a wasa biyar, daga baya ta sa kaimi ta kuma lashe Serie A na shekarar.

Juventus ta buga Gasar Serie A 14 ba tare da Ronaldo ba, ta yi nasara a wasa bakwai inda ta yi rashin nasara a hudu da canjaras uku.

Ba tare da kyaftin din tawagar Portugal, Juventus ta yi rashin nasara a Serie A da SPAL da Sampdoria da yin canjaras da Lecce.

Wasa biyar da Juventus za ta buga nan gaba:

Lahadi 1 ga watan Nuwamba Serie A

  • Spezia da Juventus

Laraba 4 ga watan Nuwamba Champions League

  • Ferencvaros da Juventus

Lahadi 8 ga watan Nuwamba Serie A

  • Lazio da Juventus

21 ga watan Nuwamba Serie A

  • Juventus da Cagliari

Talata 24 ga watan Nuwamba Champions League

  • Juventusda Ferencvaros