Champions League: Abin da kuke son sani kan wasan Juventus vs Barcelona

 • Mohammed Abdu
 • BBC Hausa

Juventus ta yi rashin naasara da ci 2-0 a hannun Barcelona a wasa na bibiyu a cikin rukuni a Gasar Champions League da suka kara ranar Laraba.

Barcelona ta fara cin kwallo ta hannun Ousmane Dembele minti na 14 da fara tamaula a birnin Turin na Italiya.

Morata ya yi ta kokarin zare kwallon farko har karo uku, amma alkalin wasa bai karba ba, saboda satar gida.

Kyaftin Lionel Messi ne ya ci ta biyu a bugun fenariti daf da za a tashi daga fafatawar, kuma ta biyu da ya zura a raga a bana.

Juventus ta karasa karawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Merih Demiral jan kati, saura minti biyar a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Barcelona tana ta daya a kan teburi na bakwai da maki shida, Juventus din tana nan ta biyu a teburin.

Daya wasan na cikin rukuni na bakwai tashi suka yi 2-2 tsakanin Ferencvarosi da Dynamo Kiev.

Barcelona za ta karbi bakuncin Dynamo Kiev ranar 4 ga watan Nuwamba a Camp Nou, a kuma ranar ce Juventus za ta ziyarci Ferencvarosi.

Ranar Asabar Barcelona ta sha kashi har gida da ci 1-3 a hannun Real Madrid a wasan hamayya na El Clasico.

Ita kuwa Juventus tashi ta yi 1-1 da Hellas Verona a wasan gasar Serie A da suka fafata ranar Lahadi.

'Yan wasan Juventus da koci Andrea Pirlo ya fuskanci Barcelona a Turin.

'Yan wasan Juventus 21:

Masu tsaron raga: Buffon da Szczesny da kuma Pinsoglio

Masu buga tsakiya: Danilo da Cuadrado da Bonucci da Demiral da De Winter da Frabotta da kuma Riccio

Masu buga tsakiya: Arthur da Ramsey da McKennie da Chiesa da Rabiot da Bentancur da Bernardeschi da Portanova da kuma Kulusevski

Masu cin kwallo: Morata da kuma Dybala

Shi ma kocin Barcelona, Ronald Koeman ya fayyace 'yan wasa 21 da za su buga wasa karawar da Juventus.

'Yan wasan Barcelona 21 da Ronald Koeman ya je da su Italiya: Dest da R. Araujo da Sergio da Alena da Griezmann da Pjanic da Braithwaite da Messi da O. Dembele da Riqui Puig da kuma Neto.

Sauran sun hada da Lenglet da Pedri da Trincao da Jordi Alba da S. Roberto da F. De Jong da Ansu Fati da Junior da Inaki Pena da kuma Arnau Tenas.

Wadanda suke yinya: Ter Stegen da Coutinho da Umtiti , yayin da Gerard Pique ba zai buga wasan ba, saboda jan kati da aka yi masa a wasa da Ferencváros.

A wasan farko da ta buga a Champions League, Barcelona ta yi nasarar doke Ferencvarosi da ci 5-1 ranar Talata, 20 ga watan Oktoba a Camp Nou.

Ita kuwa Juventus zuwa ta yi Ukraine ta doke Dynamo Kiev da ci 2-0 a ranar Talatar.

Juventus tana da kofin Champions League biyu, inda Barcelona ta lashe shi sau biyar a tarihi.

Kungiyoyin biyu sun fafata a tsakaninsu sau 13, inda Barcelona ta ci wasa hudu, Juventus ta yi nasara sau biyar da canjaras hudu.

Kofin Champions League na karshe da Barcelona ta dauka shi ne a 2015, inda ta yi nasara da da ci 3-1.

Karawar karshe da kungiyoyin biyu suka yi ita ce a kakar 2017/18

Talata 12 ga watan Satumbar 2017

 • Barcelona 3 - 0 Juventus

Laraba 22 ga watan Nuwambar 2017

 • Juventus 0 - 0 Barcelona

Ronaldo da Messi

Sai dai kuma Cristiano Ronado ba buga wa Juventus Gasar Champions League da ta yi rashin nasar a hannun Barcelona ba, saboda har yanzu yana dauke da cutar korona.

Ronaldo ya soki yadda ake gwajin annobar, kuma tuni Juventus ba ta bayyana shi cikin wadanda za su buga mata Gasar ta Champions League ba ranar Laraba.

Mai shekara 35, ya killace kansa tun lokacin da ya kamu da cutar ranar 13 ga watan Oktoba, an kuma sake gwada shi kafin Labara.

Tsohon dan wasan Real Madrid ya shirya fuskantar Barcelona da abokin hamayyarsa Lionel Messi a karon farko tun bayan 2018 da ya bar Spaniya.

Wasan karshe da Ronaldo ya buga a bana shi ne wanda tawagar Portugal ta tashi 0-0 da ta Faransa ranar 13 ga watan Oktoba kan ya kamu da cutar.

Juventus

Juventus ta dauki sabbin 'yan wasa a bana ciki har da koci Andrea Pirlo tsohon dan kwallon kungiyar, wanda ya buga mata wasa sama da 119.

Fitattu daga 'yan kwallonta sun hada da Cristiano Ronaldo da Dybala da Khedira da Chiellini da Bonucci da zakakurin gola Buffon. Sai kuma matasa da suka hada da De Ligt da Bentancur da kuma Rabiot.

Sabbin 'yan kwallon da ta dauka sun hada da Arthur Melo da Alvaro Morata da Kulusevski da Chiesa da kuma McKennie.

Barcelona

Ita kuwa Barcelona wadda a bara ba ta lashe kofi ko daya ba ta dauki sabon koci Ronald Koeman.

'Yan kwallon da ta dauka sun hada da Pedri daga Las Palmas da Matheus Fernandes daga Valladolid da Miralem Pjanic daga Juventus da kuma Sergino Dest daga Ajax.

Wasannin Juventus biyar da za ta buga nan gaba:

Lahadi 1 ga watan Nuwamba La Liga

 • Spezia da Juventus

4 ga watan Nuwamba Champions League

 • Ferencvaros da Juventus

8 ga watan Nuwamba Serie A

 • Lazio da Juventus

21 ga watan Nuwamba Serie A

 • Juventus da Cagliari

Talata 24 ga watan Nuwamba Champions League

 • Juventus da Ferencvaros

Wasa biyar da Barcelona za ta fafata nan gaba:

Asabar 31 ga watan Oktoba La Liga

 • Alaves da Barcelona

Laraba 4 ga watan Nuwamba Champions League

 • Barcelona da Dynamo Kiev

Asabar 7 ga watan Nuwamba La Liga

 • Barcelona da Real Betis

Lahadi 22 ga watan Nuwamba La Liga

 • Atl Madrid da Barcelona

Talata 24 ga watan Nuwamba Champions League

 • Dynamo Kiev da Barcelona