Lafiya Zinariya: Alamomin cutar tsananin damuwa

Bayanan sauti

A wannan makon shirin ya duba cutar tsananin damuwa.

Latsa hoton sama don sauraron shirin wanda Fauziyya Kabir Tukur ta gabatar

Sau da yawa, mutane kan shiga cikin halin damuwa da rashin walwala saboda wasu abubuwa na yau da kullum na rayuwa.

Amma idan mutum ya ci gaba da kasancewa a wannan hali na damuwa tsawon makonni ko watanni, likitoci kan ce ya gamu da cutar matsananciyar damuwa.

A kan yi wa wannan cuta kallon ƙaramin abu ko wasu ma su ce rashin hakuri ne ko rashin tawakkalin wanda ya gamu da ita.

Sai dai masana sun ce abin da mutane ba su gane ba shi ne cuta ce kamar ko wace irin cuta da kan kama wani ɓangare na jikin mutum.

Haka kuma cuta ce da ke shafar ƙwaƙwalwa da tunani wanda mai fama da ita ba shi da iko a kanta.

'Keɓewa da ƙin shiga mutane'

Dokta Ɗayyibah Shaibu, ƙwararriya a ɓangaren lafiyar ƙwaƙwalwa ta ce alama ta farko da ake gani a masu wannan cuta ita ce keɓe kai.

"Idan a baya an saba ana zama da mutum a yi hira, sai a ga yanzu ya fi son zama a ɗaki shi kaɗai ba sannan zai rage walwala.

"Ko fita za a yi gaba ɗaya mutanen gidan, mai cutar tsananin damuwa zai ce shi ba za shi ba a tafi a bar shi a gida", a cewarta.

Likitar ta ce wannan da yawan bacci ko ƙauracewar bacci da tsananin cin abinci ko rashin cin abinci inda har mutum kan ƙara ƙiba ko rage ƙiba na daga cikin manyan alamomin wannan cuta.

Amma ga mai fama da ita, tsanain baƙin ciki na babu gaira babu dalili ya ke ji a ransa.

Haka kuma, likitar ta ce cutar hawa-hawa ce. Akwai wadda ta yi tsananin da sai an daɗe ana shan magani kafin a samu sauƙi sanna akwai wadda ɗebe kewa da bayar da shawarwari kawai ke iya magance ta.

Me ke janyo cutar tsananin damuwa?

Dokta Ɗayyibah ta ce cutar tsananin damuwa na iya kama ko wane jinsi na mutane sannan ana ganinta a manya da yara duka.

Sai dai ta ce an fi ganinta a mata da matasa da suke daidai shekarun balaga.

Masana lafiyar ƙwaƙwalwa sun ce sau da yawa idan wani iftila'i ya samu mutum ne ya ke shiga halin tsananin damuwa kamar rasa wani makusanci ko kora daga wajen aiki ko haihuwa mai cike da tangarda da dai sauransu.

Dokta Ɗayyibah ta ce yanayin halittar ɗan Adam na taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan matsala.

"Wani Allah ya halicce shi da juriya. Ko da abin tashin hankali ya same shi zai daure kuma ba zai zauna masa a rai ba.

"Wani kuma ba shi da haka. Allah ya halicce shi yana da rauni kuma ba ya iya jure jarrabawa, to irinsu ne suka fi gamuwa da matsalar tsananin damuwa" a cewar Dokta Ɗayyibah.

Amma likitar ta ce wani lokaci ma haka kawai mutum kan shiga damuwa har ta zamar masa wannan cuta.

Ana warkewa daga cutar tsanain damuwa?

Dokta Dayyibah ta ce ana warkewa tsaf daga wannan cuta idan aka samu taimakon da ya kamata.

"Idan aka lura wani ya fara nuna alamomin wannan cuta, abu na farko shi ne a kai shi asibiti", a cewarta.

Akwai magunguna da hanyoyin da ake bi a asibiti ga masu fama da cutar damuwa.

"Muna ba da magunguna sannan akwai likitoci na musamman da aikinsu kawai ɗebe wa masu wanann cuta kewa da ba su shawarwari kan yadda za su tafi da rayuwarsu", in ji Dokta Ɗayyibah.

Sannan ta ce maskusantansa su riƙa jansa a jiki da nuna masa kulawa.

Duka waɗannan ne ke samar da kwanciyar hankali a tare da masu cutar har su samu lafiya.