WTO: Ƴan Najeriya na caccakar Amurka da Trump kan adawa da Ngozi Okonjo-Iweala

Ngozi Okonjo-Iweala da Trump

Ƴan Najeriya da dama sun fusata da matakin Amurka na adawa da naɗa Dakta Ngozi Okonjo-Iweala ƴar Najeriya a matsayin shugabar Ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya.

Ƴan Najeriyar sun nuna fushinsu tare da caccakar gwamnatin Trump a shafukan sada zumunta na Intanet.

Tsohuwar ministar kuɗin ta Najeriya ta samu goyon bayan jakadun ƙasashe, Haka ma ta samu goyon bayan Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka.

A ranar Laraba jekadun kasashe a ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya WTO mai mambobi 164 suka gabatar da sunan Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin sabuwar shugabar ƙungiyar.

Amma gwamnatin Trump na adawa da zaɓen Okonjo-Iweala, inda ta ke goyon bayan ƴan takara daga Koriya Ta Kudu Yoo Myung-hee.

Wannan adawar ta Amurka ya hana sanar da Ngozi a matsayin shugabar ƙungiyar, har sai an cimma matsaya kan zaɓin sabon shugaba a babban zauren ƙungiyar a ranar 9 ga Nuwamba.

Wasu na ganin duk da Trump na adawa da ƙungiyar WTO amma saboda ƙarfin Amurka tsohuwar ministar kuɗin ta Najeriya na iya fuskantar ƙalubale.

Sai dai ƴan Najeriya na da cikakkiyar fatan ganin Ngozi Okonjo-Iweala ta yi nasara duk da adawar Amurka, kamar yadda ta faru da shugaban Bankin raya Afirka Akinwumi Adesina wanda ya fuskanci adawa daga gwamnatin Trump.

Tsohon ministan sufurin Najeriya Femi Fani-Kayode ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa adawa da Ngozi ya fusata miliyoyin magoya bayan Trump a Najeriya da Afrika da kuma dubban ƴan Najeriya a Amurka.

@realFFK - Ni masoyin Trump ne wanda ke ƙaunar ya lashe zaɓe amma na yi mamakin ya toshe wa Ngozi zama shugabar kungiyar WTO.

@DeeOneAyekooto ya ce Idan har Adesina zai tsira daga adawar Amurka, Ngozi ma za ta tsira

@EvangMgbechi ya yi amfani ne da maudu'in kiran nuna wariyar Amurka ga baƙaƙen fata.

A cewarsa - Ban san dalilin da ya sa gwamnatin Trump take adawa da naɗin Dr Ngozi Okonjo-Iweala domin jagorantar Kungiyar Kasuwanci ta Duniya.

@koladegospel ya ce shi mai ƙaunar Trump ne - Amma ya kauce hanya kan adawarsa da ƴan takararsu da ta fi cancanta.

Idan dai har aka zaɓi Ngozi Okonjo-Iweala, za ta kasance mace ta farko kuma ƴar Afirka ta farko da ta taba riƙe mukamin a tarihin ƙungiyar.

Dakta Ngozi Okonjo-Iweala tana da ƙwarewa ta sama da shekaru 30 kan tattalin arziki da ci gaba, inda ta yi aiki a Afirka da Asiya da Turai da Latin Amurka.

Nagozi ta yi aiki a Bankin Duniya tsawon shekara 25 kafin zama ministar ƙudi a Najeriya.