Buhari: Shugaban Najeriya ya yi gargaɗi ga masu ƙoƙarin rusa hadin kan Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Bayanan hoto,

Buhari ya ce "da tsada" aka samu haɗin kan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga ƴan Najeriya da su guji kalamai da aikata wasu abubuwan da za su kawo cikas ga hadin kai da kuma ci gaban ƙasar.

A cikin sanarwar da Fadar Shugaban na Najeriya ta fitar ranar Laraba, Buhari ya bayyana muhimmancin haɗin kan ƙasa wanda ya ce da tsada aka same shi.

Shugaban ya faɗi haka ne yayin bikin kaddamar da alamar tunawa da mazan jiya da kuma gidauniyar naira miliyan 10 ga kungiyar tsoffin sojojin.

Shugaban wanda ya jaddada cewa karfin Najeriya ya dogara ne kan bambance-bambancenta sannan ya yi jinjina ga sojoji maza da mata da ke aikin tabbatar da tsaro wajen yaƙi da Boko Haram da ƴan bindiga masu fashin daji a sassan ƙasar.

Kazalika, ya karrama sojojin da suka kwanta dama waɗanda ya ce sun sadaukar da rayukansu a lokacin yaƙin duniya da yaƙin basasa da kuma ayyukan tabbatar da zaman lafiya a ƙasashen duniya.

"Tun samun ƴancin kan Najeriya ake fama da matsalar tsaro," in ji Buhari.

Ya ƙara da cewa barazanar tsaron ta yi tasiri a harakokin kasuwanci da saka jari da tattalin arziki da ilimi da kiwon lafiya da kuma harkokin noma tare da ci gaba da hana ƴan Najeriya walwala.

'An samu nasarori a arewacin Najeriya'

A cikin jawabinsa, Shugaba Buhari ya ce an samu nasarori a wasu yankunan arewa maso yammacin ƙasar da arewa ta tsakiya da ke fama da hare-haren ƴan bindiga masu fashin daji.

Ya ce an samu nasarori da dama a ayyukan tsaro na cikin gida a yankunan arewa maso yammaci da arewa ta tsakiya, baya ga ayyukan rundunonin Lafiya Dole da Hadarin Daji da Harbin Kunama da rundunar Whirl Stroke da Rundunar Accord da Sahel Sanity da aka kaddamar.

"Wannan ya sa harakokin yau da kullum sun dawo a yankunan da matsalar ta shafa, kuma ana ci gaba da farautar masu kai hare-hare," in ji shugaban.Buhari ya kuma ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙulla ƙawance da ƙasashe makwabtanta da aminanta domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi yankunansu.

Shugaban ya kuma yi alƙawalin cewa za a samar da kayan yaƙi na zamani ga sojojin ƙasar tare da kula da batututwan da suka shafi inganta buƙatunsu da kuma alkawalin samar da yanayin kauce wa duk wata barazanar tsaro.

Magance matsalar tsaro na cikin manyan alkawulan da Shugaba Buhari ya yi wa ƴan Najeriya a lokacin yaƙin neman zaɓensa na 2015.

Sai dai duk da hukumomi na cewa an samu nasararori a yaƙi da Boko Haram a yankin arewa maso gabas da kuma kakkabe ƴan bindiga masu fashin daji da satar mutane domin kudin fansa, har yanzu ana kai hare-hare a yankunan.