Daga baƙonmu na mako: Shin kwalliya na biyan kuɗin sabulu game da fina-finai masu dogon zango?

Dadin Kowa na cikin fina-finan dogon zango da suka fi jan hankalin masu kallo
Bayanan hoto,

Dadin Kowa na cikin fina-finan dogon zango da suka fi jan hankalin masu kallo

Kamar yadda jiki ke buƙatar abinci don ya ƙarfafa haka zuciya ke buƙatuwa da abubuwan nishaɗi don samun hutu. Abubuwan da kan nishaɗantar sun bambanta daga al'umma zuwa al'umma, haka ma a tsakanin mutane.

Wasu kan karanta littafi domin nishaɗantuwa, wasu sauraron kaɗe-kaɗe da raye-raye, wasu su yi wasa, wasu su kalli fina-finai da makamantansu.

Haka kuma wasu kan yi abubuwa sama da ɗaya don nishaɗantar da rayukansu. Wannan ne ya sanya Bahaushe kan kira "rai da dangin goro."

Wasannin kwaikwayo ko drama ko fim hanya ce ta samun nishaɗi wadda al'ummomi da yawa ke amfani da ita. A tsowon tarihin rayuwa an sami sauye-sauye bisa yadda akan yi wasan na kwaikwayo.

Kafin ci gaban zamani ya zo da hanyoyi sadarwa kamar rediyo da bidiyo akan yi wasannin ne ta hanyar ana yi ana kallo da ido, wannan shi ne asalin abin da ake kira da drama.

A irin wannan ne aka sami wasannin dandali da tashe har ya zo ga wasannin daɓe (Stage Drama).

A baya akan yi wasannin ne kai tsaye ko ta hanyar abin da aka kiyaye daga magabata tare da ɗora wani abu da zai nishaɗantar ta hanyar duba da zamani ko wuri da ake gudanar da wasan.

Daga baya aka fara rubuta wasannin kwaikwayo a bai wa 'yan wasa su karanta sannan su yi aiki da abin da suka karanto. A irin wannan tsari akan sami mai bayar da urmarni ko darakta wanda zai tabbatar da 'yan wasa sun bi tsarin da rubutun ya ɗora su.

Fim tsari ne na gudanar da kwaikwayo wanda ci gaban zamani ya haifar.

Ba a fara yin fina-finai ba sai ƙarshen ƙarni na sha-tara a lokacin da ci gaban fasahar zamani ta zo da hoto mai motsi.

A wannan lokaci an fara yin fina-finan ne a gidajen sinima inda 'yan kallo kan biya kuɗi don su kalla. Masana'antar farko da ta yi suna a wurin shirya fina-finai ita ce Hollywood ta Amurka.

Daga nan sauran sassan duniya suka ara suka yafa.

Fina-Finan Kannywood, Кyanƙashesu Da Girmansu

Kamar yadda Farfesa Yusuf Adamu ya bayyana a wata maƙalarsa, an fara ƙyanƙyasar fina-finan Hausa ne a cikin farkon shekarun Alif Ɗari Tara Da Tamanin (1980s), lokacin da wasu matasa uku a Kano - Sani Lamma da Hamisu Gurgu da Sadiya baƙar Indiya suka yi ƙoƙarin yin wasa film cikin Hausa.

A wajejen tsakiyar waɗannan shekaru (na Alif Ɗari Tara Da Tamanin), an kafa wasu kungiyoyi na wasan kwaikwayo kamar Turmbin Giwa, Gyaranya Drama da Jigon Hausa Drama wanda suka fara yin fina-finai masu dogon zango a da tashar NTA da CTV 67 (ana kiran da STV a yanzu) da gidan Talabijin na Katsina.

A wannan lokacin an yi fina-finai kamar su Bakan Gizo da Jamila da Jamilu, Hadarin Кasa da Farin Wata.

Ba na mantawa a matsayina na yaro a wancan lokacin ina mutukar son kalon waɗannan fina-finai musaman na Aminun Bose da Malam Ibrahim Mandawari Ya fito a matsayin tauraron shirin.

Wasu fina-finan da aka gudanar a wannan tsari sun hadar da Turmin Danya da Cin Amana.

Waɗannan fina-finai an gudanar da su ne a gidajen Talabijin na gwamnati kuma cikin harshen Hausa, a bisa tsari da ke da ƙarancin saɓawa al'ada; ta inda mai gida yana iya kallo tare da iyalansa da ma surukansa.

Daga shekarar 1993 fina-finan Hausa na masu Gajeran Zango suka fara kunno kai. Irin waɗannan fina-finai sun sha bamban da na farko kasancewar su ba a gidajen talabijin ake yin su ba.

Ana yin su ne a gidajen aro ko otal-otal da makarantu da makamantansu.

Kuma kasancewar sinima ta ja baya, ya sanya ana yin su ne a kaset, mai sha'awa ya saya.

Wasu cikin fina-finan sun kasance litattafai ne da aka rubutasu kafin daga baya a mayar da su fina-finai kamar su Kwabon Masoyi na Adamu Muhammad da In da so da ƙauna na Ado Ahmad Gidan Dabino da Tsutu mai wayo na Bala Anas Babinlata da Alhaki Kyuikyuyo na Balaraba Ramat Yakubu da Rikicin duniya na Ɗan'azaumi Baba Chediyar 'Yan gurasa.

Duk waɗannan na karanta su a matsayin litattafi kafin daga baya na kalle su a matsayin fim.

Fina-finan da suka biyo bayan waɗannan sun kasance fina-finai ne da za ka iya cewa ko dai an yi su ne kai tsaye ba tare da an rubuta su a matsayin littafi ba ko kuma ba a sansu a matsayin litattafai ba yayin da wasu cikinsu tatsuniyoyi ne.

Irin waɗannan fina-finai sun haɗar da Daskin da ridi da Sumbuƙa da Gagare da Allura da zare da Sangaya da Zarge.

Galibinsu an gudanar da su ne a bisa tsarin gargajiya da sanya waƙoƙi masu kama da na dandali.

Samun nasarar da waɗannan fina-finai masu gajeren zango suka yi, ya sanya kwararowar masu shiryawa da 'yan wasa zuwa Birnin Kano, wadda ake ɗauka jigo a Кasar Hausa kasancewarta mafi yawan jama'a kuma babbar cibiyar kasuwanci ta wannan al'umma.

Wannan ya sanya harkar wasan Hausa ta haɓaka a garin inda aka yi ta shirya fina-finai, mutane suka yi ta sanya jarinsu, masu fasaha kuma na yin rubutu, bayar da umarni da fitowa cikin fina-finan.

Wannan ne ya haifar da kafuwar masana'antar fim da ake kira da suna Kannywood.

Kasancewar adabin zamani na Bahaushe ya fara da kwaikwaiyo ya sanya su ma masu fim galibi ba 'ƙirƙira' fim suke ba.

Da yawansu ɗauraya ne ko jiƙo ko wanki na fina-finan waje, musamman Indiyawa.

Кari a kan haka kuma shi ne saboda kasancewar masu shirin matasa ya sanya tunaninsu bai wuce na soyayya wadda suke gani a fim ɗin Indiya.

Irin waɗannan fina-finai sun haɗa da Abun Sirri ne da Sauran Ƙiris da allura da zare da makamantansu.

Saboda cin da kasuwar take a wannan lokaci, fina-finan na fita tamkar guguwa ta koro shara; don haka mai kallo bai ma iya tuna sunayen da yawan abin da ya kalla.

Masana'anta Fim: Tsakanin Al'ada da Addini

Bayanan bidiyo,

Daga bakin mai ita tare da Bosho

Duk da cewa ba dole ne dukkan sauran al'umma su yi wa fim fahimtar haka ba, da yawan al'ummar ƙasar Hausa na buƙatar fim ɗin Hausa ya zamto ba wai kawai ya nishaɗantar ba; a a da buƙatar bayan nishaɗantarwa, fim ya faɗakar, ya ilimtar tare da yin daidai da al'ada 'Bahaushiya'.

A bisa wannan dalili ne mai kallon fim ke duba shiga da aikin 'yan wasan fim kan gudanar.

Misali mai kallo kan yi ƙorafi idan ɗan wasa ya yi shiga da ke nuna tsiraici ko sassan jiki da a al'ada akan ɓoye su.

Hakanan masu kallo kan so su ji maganganun da ake yi ba su 'shallake' tsari da ajiyar al'ada ba.

A irin wannan tsari ne wasu ke cewa fim ɗin baya wakiltar al'umma da al'ada Bahaushiya.

Kasancewar galibin al'ammar Hausawa mabiyan addinin Islama ne kuma addini ya daɗe tare da yin tasiri a al'adarsu, ya sanya komai a cikin fim ana nemansa ya zamto bisa daidaito da yadda addinin ya tsara ko al'ummar ta fahimce shi.

Misali tillas ne a ɓoye tsiraici, ba a kama yin hannu mace da namiji ko runguma ko kuma zantutukan batsa.

Maimakon haka an sami yawaita amfani da matsatsun kaya da yin amfani da zantutuka masu motsa sha'awa a cikin fina-finai da sanya mata su kaɗa jikinsu ta hanyar yin rawa da rausaya da maza da ba mazansu ba ko muharammansu ba.

A bisa wannan ƙoƙori na daidaita fim da addini ko al'ada ya sanya jihoyi, musamman Kano kanwa uwar gami ta kafa hukumar tace fina-finan Hausa, wadda a shekarun baya ta sha kafsawa da 'yan fim da shugabannin masana'antar fim ɗin.

Wannan ba karami ka-ce-na-ce ya janyo ba, wanda hakan har ya yi sanadiyar tsarewa da ɗaure wasu cikin 'yan wasa da masu shirya wasan.

Daga wurin 'yan wasan kuma sun yi ta mayar da martani a cikin fina-finai, waƙoƙi da rubuce-rubuce.

A irin wannan za mu iya tuna Marigayi Rabilu Ɗan-Ibro da yadda ya dinga shaguɓe ga shugabannin gwamnati da hukumar da ta matsa wurin abin da ta kira tacewa da tsabtace fim ɗin hausa.

Hakanan akwai wasu cikin mawaƙan masana'antar da suka rera wasu waƙoƙi kamar rabo yai rabo da hazbunallahu da makamantansu.

Wannan abin bai tsaya ga masu fim ba kawai, ya shafi har abokan tagwaitakarsu marubutan littatafan Hausa da Farfesa Ibrahim Malumfashi ya kira da "Adabin Kasuwar Kano".

Haka kuma ana yawan zargin fina-finan masana'antar da cewa an gina su ne a kan jigo guda, wato soyayya ko abin da ake kira da Nanaye.

Wannan ba ya rasa nasaba da tushen fina-finan wanda galibi ana ɗaurayo su ne daga fina-finan Hindi. Hakana kasancewar mafiya yawan masu fina-finan matasa ne, musumman limaman fari na fim wanda sun diro ne daga 'Adabin Kasuwar Kano' mai jigo guda wato soyayya.

Masana kan ce abincinka kamaninka don haka matasa galibi abin da ya fi jan hankalinsu shi ne soyayya, saboda haka ba laifi idan 'yawu zuba ta inda baki ya karkata.'

Wani suka da ake yiwa fina-finan shi ne na rashin ƙwarewa da gina labari mai ban ƙayi.

A bisa haka galibi zaren kan tsinke, sa'annan mai kallo kan iya fahimtar mai zai biyo baya ko ma ina fim zai ƙare.

Da yawan masana kan ɗora zargin hakan a bisa rashin zurfin sani na marubata, daraktoci da masu shirya fim ɗin.

'Tsirarun fuskoki ake yawan gani'

Misali, ina tuna wani zama da ƙungiya Marubuta ta Jihar Kano ta shirya da fitacciyar marubuciyar nan Hajiya Balaraba Ramat inda ta yi zargin matasan da rashin ƙwarewa har ta ce da yawa sukan ɓata maka rubutunka idan ka nemi mai da shi fim.

Hakanan na iya tuna a cikin shekarar 2006 Farfesa Abdallah Uba Adamu ya taɓa gaya mana yayin da yake koyar da mu a aji cewa ya taɓa ƙoƙarin koyawa wasu ɗalibai al'adar Bahaushe ta hanyar fim ɗin Hausa, amma sai suka yi zargin cewa al'adar ta Indiya ce kuma suka tuhumi taurarin fina-finan da rashin rai saboda kasancewar ba sa nuna damuwa ko farin ciki yadda taurari 'yan gaske' kan yi a fina-finan 'gaske'.

Wata ƙarin matsala game da fina-finan na Kannywood shi ne inda wasu tsirarun fuskoki suka zamto su kawai ake gani kumar ba masana'anta ba.

Dalilin da ya sanya na ce kamar ba masana'anta shine ita masana'antar yadda muka sani tsari ce cikakke don haka kowa yana iya hawa ya yi tafiya a kai.

Amma maimakon haka fuskoki tsiraru, musamman na maza su ne suke fitowa a fina-finan.

Don haka duk mai so yi su zai nema. Wannan ya sanya sun fara gazawa wurin gamsar da me kallo tare da jin cewa su kaɗai suka iya don haka ba su da kishiyoyo da za su zaburar da su don su yi himma kamar yadda aka saba gani a manyan masana'antu fim.

Wata matsala kuma ita ce yin fina-finan cike da gaggawa saboda kowa na son ya sami kuɗi. Galibi ɗaiɗaikun mutane ke yin fina-finan ko da sun kira kansu da kamfani.

Saboda haka babu isasshen kuɗi wanda zai sanya a yi abu da inganci.

Haka kuma babu cikakken nazari don haka sai sanya al'amura ba inda suka dace ba. Sa'annan yawan fitar fina-finan ya sanya an rasa tsari wurin kasuwanci da tallata su.

Wannan ya sanya masana'antar ta kasa samun ci gaba kamar ta abokiyar tagwaitata da ke kudancin Nijeriya.

Fina-Finai Masu dogon Zango da Sauyin da Suka Kawo

Bayanan hoto,

Labarina Series ya bi sahun fina-finan dogon zango da ke tashe a tsaknin masu kallo

Duk da a farkon fina-finan Hausa sun fara a gidajen Talabijin bisa tsarin dogon zango, tsawon shekaru sun sauka daga kan wannan.

Musamman daga shekara ta 1993 inda aka koma yin fina-finai a fefe (home Videos) kuma wannan tsari shi ya fi shura da kafuwa har kusan an manta da wancan tsari.

Kwatsam kuma sai nan baya-bayan nan, daga shekara 2015 lokacin tashoshin Arewa 24 da Tararuwa da makamantansu suka fito ungulu na neman komawa gidanta na tsamiya.

A wannan lokaci an sami ɓullar wasu fina-finai masu dogon zango da suka fara ɗaukar hankalin masu kallo. Irin wannan fina-finai sun fara ne a tashoshin da ke kan tauraron ɗan-adam, inda daga baya aka fara ɗora su a tashoshin YouTube.

Ƙarin labarai masu alaƙa

Jagora kuma fim da ya fara zuwa a wannan sabon salo shine fim ɗin Daɗin Kowa wanda har yau bai kai ga ƙarewaba duk an yanzu ya shiga zango na uku, kuma an yi kashi sama da ɗari biyu da hamsin.

Karɓuwa Daɗin Kowa ya yi ya sanya shirya wasu fina-finan masu dogon zangon kamar Kwana Casa'in da Gidan Badamasi da Labarina da Danbirni wanda dukkaninsu ana gudanar da su ne a tasoshin tauraron ɗan adam.

Bayan waɗannan kuma an sami wasu fina-finan masu dogon zango wanda suke a kan kafofin sadarwa na YouTube kamar su Izar so da Bugun zuciyar masoyi da A duniya da sauransu.

Babbar tambaya a nan ita ce ko an sami sauyi daga abubuwan da aka zargi fina-finai masu gajeren zango da su ko kuwa?

Shin idan an sami sauyi, a ina da ina ne? Idan kuma ba a sami sauyi ba ya za a yi a gyara?

Haƙiƙa idan aka yi duba ta ɓangaren kyawun labari da ƙwarewar tsara labari ma iya cewa an sami ci gaban.

Misali duk mai kallon fina-finan masu dogon zangon kamar Daɗin kowa ko Gidan Badamasi zai ga yadda marubutan ke sarrafa zaren labari ba tare da ya tsinke ba.

Hakanan za a ga yadda ake sanyawa mai kallo sha'awar ci gaba da kallo ta hanyar rikita tunaninsa game da mai zai faru a fitowa ta gaba ko shiri na gaba.

Wannan yana cikin abin da fina-finan baya suka rasa ta inda mai kallo kan iya gane inda labari zai dire tun daga fitowar farko.

A fahimtata wannan nasara ta samu ne saboda yin amfani da ƙwararrun marubuta waɗanda suka san jiya da yau ɗin rubutu kamar Nazir Adam Saleh da Bala Anas da Fauziyya D. Sulaiman da Ibrahim Birniwa da Zuwairiyya Gerei da makamantansu.

Waɗannan maruba litattafan adabi ne ba wai masu rubuta script kawai ba.

Don haka suna da ƙwarewa idan aka kamanta su da na gajerun fina-finai wadanda galibi ba su da ƙwarewa. Duk da su ma waɗannan ɗin ba ka raba su da wasu kura-kurai ko tuntuɓe.

Misali duk wanda ya kalli fim ɗin Labarina zai fahimci mai rubutun bai yi bincike game da yanayin jami'a ba. Na faɗi haka saboda shi ne tsarin da na fi ido a kai.

Hakanan za mu iya cewa ana samun ci gaba ta hanyar jigon labari ta inda yanzu za ka ga jigo kala-kala da suka shafi rayuwa, saɓanin soyayya zalla mai ƙarancin kama da ta Bahaushen mutum.

Misali duk da Gidan Badamasi cike yake da barkwanci da har ka iya cewa shi ne babban jigonsa, amma akwai rayuwar iyali da zamantakewa a gidan auri-saki na Malam Bahaushe; haka nan akwai maganar tarbiyya; da cin amana da ma yadda aikin tsaro ya ɓaci a ƙasa.

Daɗin Kowa sha kundum ne wurin game jigogi kamar maganar tsaro, ilimi da karantarwa (almajiranci), cin haci da rashawa; zamantakewar iyali da al'umma, rayuwar birni ko bariki da makamantansu.

Kwana Casa'in ya fara ne da siyasa, amma yanzu ban san inda ya dosa ba, ko dai dan na daina kallo ko kuma zaren bai saƙu irin na biyun da na ambata kafinsa ba.

Wata nasara da aka sake samu ita ce na yin amfani da sabbin fuskoki da jarumai, ta inda yanzu matasa kan shigo su kuma taka rawar da dama ta su ce.

Wannan ya saɓawa baya inda wasu ke fitowa ko da yaushe.

Wannan kuma ya faru domin masu shirya fim ɗin kan tallata ne da ɗaukan waɗanda suka dace da rawar da suke so a taka a fim.

Yanzu kam tabbas mun fahimci ko cewa magaji ma zai iya gaje gwani in ya kau ko ya gaza.

Ta fuskar daidaito da al'adar Bahaushe kuwa, idan muka duba waɗannan fina-finai masu dogon zango muna iya cewa an sami ci gaba a wani ɓangaren, a wani sashen kuma ana nan jiya ya yau.

Misali, mun daina ganin waƙa da rawa da samari da 'yan mata kan ɓuya su yi a bayan bishiya, wanda wannan ya rusa zaton masu cewa sai an yi rawa za a kalli fim.

Sa'annan a waɗannan fina-finai ana amfani da gida da ma gari da ya fi kama da irin namu.

A waɗancan galibi otel da gidan attajirai ake nuna mana, amma yanzu za mu ga ƙauye da birni da talaka da akurkinsa, da mai kuɗi da shigifunsa.

Amma kuma game da sittira ka iya cewa, har yanzu da sauran rina a kaba musamman a fina-finan na YouTube.

Hakan bai rasa nasaba da rashin tace su da akan yi. Haka nan waɗannan fina-finai suna ɗauke da wasu abubuwa na taɓara da rashin kunya.

Kammalawa

Duba da abin da ya gabata za mu iya cewa fim ɗin Hausa ya fara da dogon zango kafin ya koma mai gajere zango, wanda a lokacin ne ya shahara har ya kafa masana'anta ta kansa.

Daga baya-bayan nan da alama ungulu ta fara komawa gidanta na tsamiya.

A lokacin ganiyar finai-finai masu gajeren zango ana zargin masu gudanar da fim ɗin da gazawa wurin wasu abubuwa kamar cika da kyan jigo da rashin daidaito da addini ko al'ada da rashin sauyin fuska.

Duk waɗannan sun sami inganci a fina-finai masu dogon zango idan aka kamanta da gajerun.

Sai dai har yanzu da buƙatar daidaita fina-finan da haƙiƙanin al'ada da ingantasu ta inda wanda ba Bahaushe zai iya kallonsu ya yi nazari cikin rayuwarsa, kasancewa fim adabi, yana nuna kasancewarsa hoto ko mudibi na rayuwa.

Wannan maƙala ce ta musamman daga baƙonmu na mako: Murtala Uba Mohammed (PhD), malami ne a Sashen Jogorafi na Jami'ar Bayero ta Kano kuma mamba a ƙungiyar marubuta ta ƙasa (ANA) reshen Jihar Kano. Murtala yana da sha'awar rubuce-rubuce cikin Harshen Hausa da na Turanci.