#ENDSARS: Ku kalli bidiyon bayani kan yi sace-sacen ban mamaki da aka yi a Najeriya

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Zanga-zangar #ENDSARS ta haifar da abubuwa da dama a Najeriya, ciki har da fasa rumbunan abinci domin kwasar abincin da ke ciki, da kuma shiga gidajen wasu 'yan majalisa da manyan hamshaƙan gwamnati domin kwashe kayan da ke ciki.

Amma abu mafi ban mamaki shi ne yadda aka dinga satar wasu kayayyaki da ba dangin abinci ba kamar sndar sarauta da allon sunan birni da gilashin mutum-mutumi da sauransu.

Ga dai Halima Umar Saleh da sharhi kan yadda lamarin ya kasance.

Ɗaukar bidiyo da tacewa: Yusuf Yakasai