Bidiyo: Mata Hausawa da ke aikin kanikanci a Kano

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Kanikancin aiki ne da ake ganin na maza, amma kuma a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, aikin ya karɓi wasu mata da ke kanikancin mota.

A yankin arewacin Najeriya, aikin kanikanci ga mace wani sabon abu ne da ba a saba gani ba.

Duk da dalilai da suka shafi addini da al'ada, hakan bai sanyaya gwiwar wasu mata ba da suka rungumi sana'ar ta kanikanci.

Wasu ƙarin bidiyo da za ku so ku kalla