Bidiyo: Abin da ya jawo ƙasashen Musulmai suka juya wa Faransa baya

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyo:

Wata fafutuka da aka fara a intanet a wasu ƙasashen Musulmai ta ƙaurace wa kayayyakin da Faransa ke samarwa ta samu goyon baya sosai daga shugaban ƙasar Turkiyya Recep Erdogan.

Ya yi kira daga Turkawa da ka da su sayi kayayyakin da Faransa ke samarwa tare da zargin Shugaba Emmanuel Macron na amfani da kalaman ƙiyayya kan Musulunci.

Mun yi waiwaye kan yadda dukkan abin ya kasance.

Wasu bidiyon da za ku so ku kalla