...Daga Bakin Mai Ita tare da 'Stephanie' ta Daɗin Kowa

Latsa hoton sama don kallon bidiyon:

Daga Bakin Mai Ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zalla.

A wannan kashi na 21, shirin ya tattauna da fitacciyar tauraruwar da ke fitowa a shirin Daɗin Kowa na talabijin wato Sarah Aloysious da aka fi sani da Stephanie, inda ta amsa tambayoyin da za su sa ku dariya.

Sarah haifaffiyar jihar Adamawa ce amma ƴar asalin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Ita ƴar ƙabilar Margi ce kuma a Maiduguri ta taso. A can ta yi karatu tun daga firamare har zuwa Kwalejin Kimiyya ta Ramat Polytechnic.

A yanzu tana karatun digiri ɗinta a Jami'ar Karatu daga gida ta Najeriya a Kano wato Noun.

Baya ga shitin Dadin Kowa, Sarah ta ce ta fito a wasu fina-finan Kannywood da ba su fito kasuwa ba tukunna kamar su Hikima da Ameer da Ƙaddararmu ce, sannan tana da kamfani nata na kanta da take shirya fina-finai da za su fito nan gaba.

Ɗaukar bidiyo da Gabatarwa: Yusuf Ibrahim Yakasai

Tacewa: Yusuf Yakasai da Fatima Othman

Ga wasu na baya da za ku so ku kalla