Gane Mani Hanya: Yadda aka ƙirƙiri rundunar SWAT da yadda za ta yi aiki a Najeriya

A wannan makon, Shirin Gane Mani Hanya ya tattauna da Ministan Ma'aikatar 'Yan Sanda a Najeriya kan yadda aka ƙirƙiri rundunar SWAT da yadda za ta yi aiki.

Muhammad Maigari Dingyadi ya ce 'yan sandan sabuwar rundunar za su karɓi horo na tsawon wata ɗaya.