Harin Zabarmari: Malaman addini sun ce Buhari ya gaza kan matsalar tsaro

Maharan sun kashe akalla mutum 43 a jihar Borno a karshen mako
Bayanan hoto,

Maharan sun kashe akalla mutum 43 a jihar Borno a karshen mako

Da alama Malaman addinin Musulunci a Najeriya sun soma dawowa daga rakiyar Gwamnatin Muhammadu Buhari sakamakon abin da suke cewa rashin mayar da hankali wajen magance matsalar tsaro da ta addabi musamman Arewacin kasar.

Malamai da dama da BBC ta tattauna da su sun ce dole gwamnatin Shugaba Buhari ta zage damtse don shawo kan matsalar tsaron ƙasar idan ba haka ba Allah zai yi fushi da ita.

Wannan jan kunne na zuwa ne bayan waɗanda ake zargi mayaƙan Boko Haram ne sun kashe aƙalla manoma 43 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Malam Aminu Ibrahim Daurawa, fitaccen malamin da ke jihar Kano, ya shaida BBC cewa ya zama wajibi Shugaba Buhari ya sauya salo wajen tunkarar matsalar tsaron da ke addabar arewacin ƙasar.

"Muna kira ga shugabannin da su ji tsoron Allah su san cewa zai tambaye su rayukan mutane miliyan 200 da suke rayuwa a Najeriya. Kuma alƙawari suka yi mana cewa za su yi iya yin su su ga cewa sun ɗauki mataki a kan harkar tsaro da harkar noma da kiwo da kuma harkar cin hanci da rashawa," in ji shi.

Ya ƙara da cewa: "Waɗannan abubuwa guda uku yanzu sun ƙara tabarbarewa sun lalace a wannan kasa" don haka ya zama wajibi a shawo kansu.

Shi ma Malam Halliru Maraya ya ce a bayyane take ƙarara cewa gwamnatin Buhari ta gaza kare rayukan al'ummar ƙasar.

"Ita kanta gwamnati babban aikinta shi ne tsare rayuka da dukiyoyin jama'a da samar da walwala ga jama'a kamar yadda tsarin mulkin ƙasa ya faɗa. Wannan ya nuna cewa babban aikin gwamnati a fili ta gaza. A zahiri gwamnati ta gaza," in ji shi.

A nasa ɓangaren, Malam Musa Yusuf wanda aka fi sani da Asadus-Sunnah, ya mayar da hankali ne kan malaman da suka yi shiru duk da kashe-kashen da ke faruwa a arewacin Najeriya.

A cewarsa: "Duk wani malami da hau mumbari na Juma'a da bai fito ya yi huɗuba a kan wannan matsalar rashin tsaro ba, to wannan malamin maciyin amanar al'umma ne da addinin Musulunci. Babu wani dalili da zai sa ana kashe mutane ka hau mumbari kana yi musu huɗuba a kan muhimmanci sadaka ko azumin nafila.

Ya ja kunnen malaman da suka yi gum da bakunansu cewa idan suna ganin wannan matsala ba ta shafe su yanzu ba, su sani cewa idan ta ci gaba da faruwa watarana za ta zo kansu.

A lokacin mulin Shugaba Goodluck Jonathan ma, malaman sun yi ta addu'o'i da ma alqunutu yayin da matsalar rashin tsaro ta addabi arewacin Najeriya.

Sai dai tun da Shugaba Buari ya hau kan muli ba kasafai ake jin muryoyinsu ba idan ban da yanzu da suka yunƙori domin gaya wa Shugaba Buhari gaskiya.