Eid ElMaulud: Wasu hotunan yadda aka yi bikin Maulidi a faɗin duniya

Wasu 'yan mata musulmai na raira waka yayin bikin Maulidin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad a masallacin Anwar da ke Addis Ababa, babban birnin Ethiopia a ranar 29 ga watan Oktoba 2020.
Bayanan hoto,

Wasu 'yan mata musulmai na raira waka yayin bikin Maulidin murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad a masallacin Anwar da ke Addis Ababa, babban birnin Habasha a ranar 29 ga watan Oktoba 2020.

Bayanan hoto,

Ranar 12 ga watan Rabiul Awwal ake bikin bikin Maulidi domin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad.

Bayanan hoto,

Gwamnatocin ƙasashe da dama kan bayar da hutu ga ma'aikata da makarantu domin bikin ranar Maulidi

Bayanan hoto,

Mutane na tafiya a wani ƙayataccen wuri da ake bikin Maulidin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad a Lahore, Pakistan a ranar 29 ga watan Oktoba 2020.

Bayanan hoto,

Shugaban ƙasar Afghanistan Ashraf Ghani yana bayani yayin bikin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad a Kabul, babban birnin Afghanistan ranr 29 ga watan Oktoba 2020

Bayanan hoto,

Mutane da dama ne suka halarci wani biki a Azamiya a wani bangare na murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad a Bagadaza babban birnin Iraqi a ranar 29 ga watan Oktoban 2020. An kuma gabatar da shirin a masallacin Abu Hanifa.

Bayanan hoto,

Wasu mazaje na yin girki ga waɗanda za su halarci taron bikin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad a birnin Krueng Barona Jaya a lardin Aceh a ƙasar Indonesia a ranar 29 ga watan Oktoba 2020

Bayanan hoto,

Shugaban ƙasar Turkiyya Racep Tayyib Erdugan yana bayani lokacin buɗe wani taron biki na mako guda domin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad a dakin taron kasar na Bestepe na cibiyar raya al'adu da ke Ankara babban birnin ƙasar Turkiyya a ranar 29 ga watan Oktoba 2020.

Bayanan hoto,

Yaran Falasɗinawa sun halarci bikin Maulidin Annabi Muhammadu a wajen ginin masallacin al-Aqsa wuri na uku mafi tsarki ga musulmai a duniya, da ke tsohon birnin Jerusalem a ranar 29 ga watan Oktoban 2020.

Bayanan hoto,

Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayin bikin Maulidin Annabi Muhammad da ya gudana a birnin Bauchi a arewacin Najeriya a ranar 28 ga watan Oktoban 2020.

Bayanan hoto,

Taron mutane a cikin daren ranar 28 ga watan Oktoba 2020 a jihar Bauchi a arewacin Najeriya, lokacin da suka halarci bikin Maulidin Annabi Muhammad