An yanke wa ƴan Mali biyu hukuncin kisa kan harin ta'addancin 2015

Dakarun kasar Mali sun yi wa wajen otal din Radisson Blu kawanya a ranar 20 ga watan Nuwambar shekarar 2015.
Bayanan hoto,

A cikin watan Nuwamban 2015 ne 'yan bindiga suka kai hari a otal din Radisson Blu a birnin Bamako, inda suka yi garkuwa da mutane 170 tare da hallaka mutane 20

Wata kotu a kasar Mali ta yanke wa wasu maza biyu hukuncin kisa kan hare- haren da suka kai kan wasu 'yan kasashen waje a birnin Bamako a shekara ta 2015.

Mutum a ƙalla 25 ne suka rasa rayukansu, lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari a wani gidan rawa a Bamako babban birnin kasar a watan Maris na cikin shekarar, da kuma otal din Radisson Blu cikin watan Nuwamba.

Ɗaya daga cikin wadanda aka gurfanar din ya shaida wa kotun cewa yana 'alfahari' da rawar da ya taka wajen kai harin, wanda ƙungiyar masu jihadi ta dauki alhakin kaddamarwa.

Ba kasafai ake samun irin wannan da ta shafi kungiyar masu jihadi ba a kasar, da ke fada da masu tada kayar baya tun a shekara ta 2012.

Sojojin Faransa na taimaka wa dakarun kasar ta Mali, amma kuma gwamnatin ta gaza samun karfin ikon daukacin tafiyar da kasar.

Fawaz Ould Ahmeida, wani ɗan tayar da ƙayar baya ɗan asalin ƙasar Mauritaniya, ya ce ya kai hari a wurin shaƙatawa na La Terrasse, a matsayin ɗaukar fansa kan wallafa zanen barkwancin da ke yinɓbatanci ga Annabi Muhammadu da mujallar nan ta ƙasar Faransa Charlie Hebdo ta yi.

'Yan kasar Mali uku, da ɗan kasar Faransa, da ɗan ƙasar Belgium ɗaya ne suka rasa rayukansu a harin. An yanke wa shi ma ɗan kasar Mali kuma abokin tafiyar Ahmeida Sadou Chaka hukuncin kisan, kan hannu da yake da shi wajen kai harin.

Bayanan hoto,

An cafke Fawaz Ould Ahmeida a wajen birnin Bamako a shekara ta 2016

An dai zargi Ahmed da kitsa harin na otal din Radisson Blu.

Wasu 'yan bindiga biyu ne suka yi garkuwa da baƙi 170 da ma'aikatan otal din har na tsawon sa'oi tara, inda suka hallaka akalla mutane 20 kafin jami'an tsaro su kawo dauki a wurin.

'Yan kasar Mali tara, da dan kasar Russia ma'aikacin jirgin sama, da jagororin kamfanin gine-gine na kasar China, da wani dan siyasar kasar Belgium da kuma wani Ba Amurke ma'aikacin agaji na cikin wadanda suka rasa rayukansu.