Eid Maulud: Muhimman abubuwan da ake so Musulmi ya yi a ranar Maulidi

Masallacin Madina

Al'ummar Musulmi da dama ne yau a faɗin duniya ke murna da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammadu (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.)

Musulmai da dama sun yi amannar cewa a watan Rabiu'l Awwal, aka haifi Annabi Muhammadu (SAW).

A irin wannan rana ce Allah (SWA), ya yi wa halittarsa kyautar da ta fi kowacce irin kyauta daraja wato Manzon Allah SAW, kamar yadda Musulunci ya bayyana.

Malamai sun ce al'ummar Musulmai za su iya yin dukkan abin da suke gani Allah da Manzonsa sun yarda a yi, sai su yi domin nuna murnarsu da zagayowar wannan rana.

Shin to me ya kamata a yi a wannan rana?

Sheikh Halliru Maraya, malamin addinin Musulunci a Kaduna ya shaida wa BBC cewa, za a iya tara mutane a yi musu lakca a game da halayen Manzon (SAW) domin su yi koyi.

Malamin ya ce,"Dan kasuwa zai iya jin yadda Annabi ya yi kasuwanci domin ya yi koyi, haka masu aure su ji yadda Annabi ya yi zaman aure a yi koyi, su ma shugabanni su ji yadda Annabi ya yi shugabanci su ma su yi koyi".

Sheikh Halliru Maraya, ya ce baya ga lacca, Musulmai za su iya ziyartar asibiti da niyyar taimakawa da kuma duba marasa lafiya don a nuna wannan rana ce da aka samu rahama.

Malamin ya ce,"Baya ga zuwa asibiti, za a iya zuwa gidan yari, ko a dafa abinci a rabawa mabuƙata, da sadar zumunta ta hanyar ziyara ko a kira waya domin a sada zumunta".

Tun yaushe aka fara Mauludi?

Sheikh Halliru Maraya, ya ce an fara maulidi ne tun hijira na da shekara 604, wanda ya fara yin sa shi ne Sarkin Erbil na wancan lokaci wato Mozaffar ad-Din.

Erbil a yau tana cikin Iraƙi, kuma babu a inda aka ambata a Ƙur'ani ko Hadisi ko kuma malamai su yi ijma'i a ce sai Annabi ya yi kaza ne abin ya zama halal.

Malamin ya ce, babban abin da za a yi la'akari da shi, shi ne Allah ya hana? Ko Annabi ya hana?

Sheikh Halliru Maraya, ya ce ƙur'ani ya ce abin da Manzon Allah ya kawo muku ku riƙa, haka abin da ya haneku ku guje masa.

Ƙarin bayani kan mauludi

Al'ummar Musulmai dai kan yi hidima a wannan lokaci, inda a kamar a Najeriya musamman a jihohin arewacin ƙasar, makarantun allo ko na Islamiyya kan shirya mauludi ta hanyar ƙayata waje a gayyaci manyan baƙi a zo a bai wa ɗalibai karatu da waƙoƙi na yabon Annabi su zo su rinƙa yi.

Wata al'ada kuma za ka ga a wannan rana a kan dafa abinci da nama musamman kaji a raba gida-gida na maƙwabta kamar ranar sallah.

A wani lokaci ma har ɗinki ake yi wa yara don su sanya sabon kaya kamar sallah.

Ga wasu mutanen kuma a kan shirya taron lakca inda za a gayyato malamai su yi wa'azi.