WTO: Me ya sa Amurka ta ƙi nuna goyon-bayanta ga jagorancin Ngozi Okonjo-Iweala

Ngozi Okonjo Iweala for di WTO

A ranar 9 ga watan Nuwamba 2020, ake sa ran Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya ta sanar da Dr Ngozi Okonjo-Iweala ta Najeriya a matsayin sabuwar shugabarta.

Idan har Ngozi Okonjo-Iweala ta ɗare wannan kujera, za ta kasance mace ta farko kuma 'ƴar Afirka ta farko da ta taɓa riƙe muƙamin a tarihin ƙungiyar da ta kai shekara 25 da kafuwa.

Ngozi na fafatawa ne da Ministar Kasuwanci ta Koriya Ta Kudu, Yoo Myung-hee a zagayen ƙarshe na takarar kujerar shugabancin Ƙungiyar.

Yanzu haka jakadun ƙasashe a Ƙungiyar Cinikayya ta WTO sun gabatar da sunan tsohuwar ministar kuɗin Najeriya a matsayin sabuwar shugabar ƙungiyar.

Sai dai akwai ƙasa guda wato Amurka da ta nuna adawa da zaɓen Okonjo-Iweala, inda take goyon bayan 'ƴar takara daga Koriya Ta Kudu Yoo Myung-hee.

Me ya sa Amurka ta ƙi mara baya ga Okonjo-Iweala?

Wakilin BBC kan harkokin kasuwanci Andrew Walker, ya ce Amurka ta nuna ta fi son Myung-hee saboda "ƙwarewarta a fannin cinikayya da kuma irin rawar da za ta iya takawa a ciyar da ƙungiyar gaba".

Babu dai wata hujja da suka bayar kan ƙin mara wa Okonjo-Iweala baya.

Amma dai za a ci gaba da tattaunawa har zuwa lokacin da za a fitar da sakamakon ƙarshe.

Abin da Okonjo-Iweala ta ce

Mai magana da yawunta a WTO ya ce: Dr Ngozi ta yi murnar goyon-bayan da ta samu ko aka nuna mata tsakanin mambobin WTO.

Ta ji dadin aminta da ita da kuma muradan da take da su wajen sake gina WTO da dawo da ƙungiyar kan turba.

"Dr Ngozi na dakon ranar 9 ga watan Nuwamba lokacn da kwamitin zai sanar da matsayarsa da amincewa da naɗinta a matsayin sabuwar shugabar ƙungiyar."

Me zai faru nan gaba?

Dan jaridar Najeriya Oluwamayowa Tijani da ke bayar da rahoto kan halin da ake ciki ya shaida wa BBC cewa, har yanzu akwai sauran aiki wajen tabbatar da wannan kujera ga Okonjo-Iweala duk da cewa ita ke da rinyaje a ƙuri'u.

A yanzu dai ta tabbata ta lashe ƙuri'ar ɗare wannan kujera, sai dai ya zama tilasta sake samun amincewa daga ƙasashe mambobin WTO, kasancewa suna da yarjejeniyar da ta kafa su.

Ƙungiyar ta shiga tattaunawa domin yanke hukunci ko za su yi amfani da sakamakon da zaɓe ya ba su ko akasin haka.

"Matsalar a yanzu ita ce Amurka ba ta son ta, ta fi son 'ƴar Koriya Ta Kudu. Don haka akwai yiwuwar Amurka ta nemi haɗin-kan abokanta wajen cimma manufarta.

Duk da cewa ita ce mai rinjayen ƙuri'a akwai yiwuwar ta rasa wannan dama saboda dalilai na yarjejeniya da tsarin kafuwar ƙungiyar, in ji Tijani.

A cewar Paul Nwabuikwu, wanda shi ne kakakin Okonjo Iweala, zai kasance abun farin ciki a ce nasu ke kan wannan kujera.

Ya ce, "Nasararta za ta kasance labari mai daɗi ga Afirka. A tsawon lokaci, ƙasashe masu tasowa da matalauta na yawaita ƙorafe-ƙorafe kan rashin jindadin dokokin cinikayyar duniya.

WTO ƙarkashin shugabancinta za ta taimaka wajen sake gina Afirka da ƙarfafa gwiwa da sake fito da hikima da bunkasa harkokin kasuwanci".

Me Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya ke yi?

Ƙungiya ce ta Cinikayya wanda kuma gwamnatocin ƙasashe ke ƙula da yarjejeniyar kasuwanci. Wuri ne da gwamnatocin ƙasashe daban-daban ke shawo kan matsaloli ko rikicin kasuwanci da ke tsakanin mambobinsu.

Gwamnatocin ƙasashe ke tafiyar da harkokin WTO da kuma tsayar da shawara. Ministoci a ƙungiyar na hadu wa a ƙalla sau guda a cikin shekara biyu ko wakilansu da ke haduwa akai-akai a Geneva.