Lai Mohammed: Gwamnatin Najeriya na kuka da shafukan sada zumunta

Lai Mohammed
Bayanan hoto,

Ministan yaɗa labaran Najeriya Lai Mohammed ya ce kafofin sada zumunta za su iya halaka Najeriya

Mahukunta a Najeriya sun ce akwai buƙatar a taƙaita wasu al`amuran da suka shafi harkokin sada zumunta na zamani a kasar.

Ministan yaɗa labaran ƙasar, Lai Mohammed ya ce sanya ka`idar za ta taimaka wajen rage yaɗa labaran ƙarya.

Gwamnatin Najeriyar na wannan yunkurin ne mako guda bayan zanga-zangar da aka yi a kasar, inda matasa suka yi amfani da kafofin sada zumunta na Twitter da Intagram da kuma Facebook wajen yaɗa wasu hotunan bidiyo na wasu harbe-harben da suka zargi sojoji, zargin da rundunar soji ta ƙaryata.

Lai Mohammed ya bayyana haka ne lokacin da yake kare kasafin kuɗin ma'aikatarsa a gaban wani kwamitin Majalisar Wakilai, inda ya ce ɗabi`ar baza labaran ƙarya ta shafukan sada zumunta babbar barazana ce ga ƙasa irin Najeriya.

Ministan ya ce duk da turjiya daga sauran jiga-jigan da lamarin ya shafa, akwai bukatar a ɗauki mataki na sanya ka'idojin amfani da shafukan sada zumunta da intanet.

"Ina shaida muku cewa idan ba mu shata ka'idoji ba waɗannan shafukan sadarwar za su halaka mu." in ji Lai Mohammed.

Ya kuma ce ba kushe shafukan sada zumunta suke yi ba baki ɗaya ba, suna kuka ne saboda kara-zube suke.

"Muna magana ne a kan illolinsu. Kuma ba ƙasashen da ke mulkin gurguzu kaɗai ba ne suke ɗari-ɗari da su ba, hatta Amurka tana taka-tsantsan," a cewarsa.

Sai dai wasu daga cikin `yan majalisar sun soki kalaman ministan, suna masu nuna rashin amincewarsu da aniyarsa, inda suka cewa su ma shafukan sada zumuntar da amfaninsu.

Wasu ƴan majalisar sun bayar da misali da rawar da suke takawa wajen nuna wa duniya gaskiyar kwasar ganima ko fasa wuraren ajiyar da wasu suka yi a Najeriya bayan zanga-zangar EndSARS.

Gwamnatin Najeriya na da'awar yi wa masu amfani da shafukan sada zumunta na intanet linzami ne mako guda da kammala zanga-zangar EndSARS.

Matasa sun yi ta amfani da shafukan sada zumunta wajen yaɗa hotunan bidiyo na abubuwan da suka faru a sassan ƙasar, ciki har da batun buɗewa musa zanga-zanga wuta da ake zargin jami`an tsaro da yi.

Sai dai kamar yadda yunkurin sanya ka'idar ya fuskanci turjiya a wajen wasu ƴan majalisar, ra`ayi ya bambanta a tsakani wasu masu amfani da shafukan sada zumuntar na intanet.

Wasu ƴan ƙasar na ganin yadda aka yi amfani da shafukan wajen yaɗa labaran ƙarya a lokacin zanga-zangar ya kamata gwamnati ta yi dokar da za ta hukunta masu yaɗa labaran ƙarya.

Wasu kuma na ganin hakan zai zama wata silar daƙile ƴancin faɗin albarkacin bakin al'umma.

Me ƴan Twitter ke cewa?

Kalaman Lai Mohammed sun ja hankali, musamman yadda aka riƙa danganta Najeriya da kasashe kamar China da suka takaita amfani da shafukan sada zumunta.

A cewar Ejikem gwamnati ta gano cewa ba za ta iya juya su ba da duniya a kafofin yada labaran da take da iko da su.

Omojuwa ya ce idan har Lai Mohammed na nufin Najeriya ta takaita amfani da shafukan sada zumunta kamar China, to duk wani dan Najeriya da ya damu da ƴancinsa dole ya damu. Saboda China ta yi manyan abubuwa, keta haƙƙin ɗan Adam da ƴancin faɗin albarkacin baki ba ya cikinsu.

Mahukunta a Najeriyar sun sha kwaramniya da ƴan kasar a kan sanya ka`idojin amfani da shafukan sada zumunta.

A shakarar 2015 da 2019, an yi irin wannan yunƙurin amma ba a cimma nasara ba.