Charlie Hebdo: Turkiyya za ta shigar da ƙara kan zanen ɓatanci ga Erdogan a Faransa

Erdogan da Macron

Turkiyya ta yi barazanar daukar mataki na shari'a da diflomasiyya kan Faransa bayan da mujallar Charlier Hebo ta wallafa zanen Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

Zanen ya nuna shugaban ƙasar Turkiyyan yana ɗage mayafin wata mata.

Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce masu shigar da ƙara sun ƙaddamar da wani bincike a hukumance kan mujallar barkwancin.

Tashin hankali tsakanin Faransa da Turkiyya ya ƙaru bayan da Shugaba Emmanuel Macron ya sha alwashin ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki kan masu ƙarfin kishin Islama.

Mista Erdogan ya yi kira ga Turkawa da su ƙaurace wa kayayakin da Faransa ke samar wa sannan ya ce Mista Mcaron na buƙatar a yi masa gwajin lafiyar ƙwaƙwalwa.

Lamarin ya yaɗu a sauran ƙasashen duniya, inda aka dinga ƙaurace wa kayayyaki da kuma zanga-zangar nuna adawa da Faransa da aka dinga yi a ƙasashen da Musulmai suka fi yawa da suka haɗa da Bangladesh da Kuwait da Jordan da Libiya.

Shugaba Macron ya bayyana cewa an kashe malamin nan Samuel Parte ne sakamakon Musulmai na son ƙwace musu rayuwarsu, amma hakan ba zai sa Faransa ta daina zane-zanenta ba, in ji Mista Macron.

Nuna hoto ko kuma yin zanen batanci ga Annabi, saɓo ne a wurin Musulmai.

Faransa dai na ɗaukar ra'ayin waɗanda ba su da addini da muhimmanci. Ƙasar ta bayyana cewa take haƙkin faɗin albarkacin baki don saboda wani rukunin mutane abu ne da zai iya kawo cikas ga haɗin kan ƙasar.

Ta ya Turkiyya ta mayar da martani ga zanen barkwanci na Charlie Hebdo?

Zanen barkwanci da aka yi kan Mista Erdogabn ya fusata gwamnatin Turkiyya.

Daraktan watsa labarai na ƙasar, Fahrettin Altun ya bayyana cewa: "Charlie Hebdo ta wallafa wasu jerin zane-zanen barkwanci da ke nuni ga shugaban ƙasarmu. Muna Allah wadai da wannan zanen da ta wallafa a yunƙurinta na yaɗa wariyar al'ada da ƙiyayya.

Mataimakin Shugaban ƙasar. Fuat Oktay ya yi kira ga ƙasashen duniya su ɗaga muryoyinsu kan wannan "abin kunyar".

"Ba za ku iya mayar da mutane wawaye ba da sunan 'yancin faɗin albarkacin baki," kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter.

Haka kuma, wata mujalla da ke goyon bayan gwamnatin Turkiyyar ta wallafa wasu jerin zanen barkwanci a shafinta na Twitter inda take caccakar Shugaban Faransa Emmanuel Macron da kuma Mujallar Charlie Hebdo.

Mujallar Charlie Hebdo ta daɗe da zama abin ce-ce-ku-ce musamman zanen da ta ke yi na batanci ga musulmi.

A 2012, an kashe mutum 12 a wani hari da aka kai a ofisoshin mujallar da ke birnin Paris. A shekarar dai, Rasha ta caccaki mujallar inda take zarginta da yin zanen barkwanci kan hatsarin jirgin sama na Sinai wanda mutum 224 suka mutu.

Ko a 2016 ma sai da suka yi wani zanen barkwanci da ke nuna mutanen da girgizar ƙasa ta rutsa da su a Italiya, lamarin da ya jawo fushi da tayar da jijiyoyin wuya.