#ENDSARS: Sace-sacen ban mamaki da aka yi a Najeriya cikin mako ɗaya

Bayanan bidiyo,

Ku kalli bidiyon bayani kan yi sace-sacen ban mamaki da aka yi a Najeriya

Latsa alamar lasifika domin kallon irin kayayyakin da aka sata na ban mamaki

Zanga-zangar #ENDSARS ta haifar da abubuwa da dama a Najeriya, ciki har da fasa rumbunan abinci domin kwasar abincin da ke ciki, da kuma shiga gidajen wasu 'yan majalisa da manyan hamshaƙan gwamnati domin kwashe kayan da ke ciki.

Gwamnatin ƙasar ta yi Allah wadai da yunƙurin da waɗannan matasan ke yi na aikata wannan sata, inda da dama aka fi ɗibar kayan abinci da ke rumbunan gwamnati da na 'yan kasuwa.

Sai dai duk a cikin waɗannan sace-sacen, akwai wasu abubuwan da aka sace na ban mamaki da ake zaton ba yunwa ba ce za ta sa ɓarayin yin hakan, sai don son rai.

Abubuwan ban mamakin da aka sace sun haɗa da:

Sandar girma ta Oba na Legas

Washe gari bayan harbin masu zanga-zanga a Lekki da ke Legas, wasu da ake zargin cewa 'yan daba ne suka afka gidan Oba na Legas inda suka lalata gidan tare da awon gaba da wasu muhimman abubuwa.

Cikin abubuwan har da sandar girma ta Oba na Legas wadda ya gada tun kaka da kakanni.

A lokacin da suka afka gidan, sun so su ƙona gidan sarautar amma sojojin da ke wurin suka hana a yi hakan.

Irin wannan lamarin ya fara ne a Legas, ya bazu zuwa wasu jihohi kamar Oyo da Kwara da Kaduna da Filato da Adamawa da birnin Abuja da wasu jihohin

Sace riga da hular alƙali

Wasu da ake zargin 'yan daba ne da suka kai hari Kotun Tarayya da ke Igbosere sun ƙona ta tare da sace wasu kayayyakin da ke cikin kotun.

An ga wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta inda aka ga ɗaya daga cikin 'yan daban sanye da hula da kuma rigar alƙali ta kotun yayin da lamarin ke faruwa.

Sauran abubuwan da aka sace a kotun sun haɗa da firij da kujeru da na'urar sanyaya ɗaki, haka kuma an bayyana cewa kotun na daga kotu mafi daɗewa a tarihin Najeriya.

Sace Taraktoci

Kungiyar tallafa wa manoma ta arewa maso gabashin Najeriya, NECAS, ta ce an sace taraktoci 110 a ma'adanar kayayyakin noma a shelkwatar ƙungiyar da ke birnin Yola na Jihar Adamawa.

A farkon makon nan ne dai bidiyon yadda matasa ke tura taraktoci ɗauke da sunan ƙungiyar ta NECAS ya yaɗu a shafukan sada zumunta bayan matasan sun yi wawason kayan abinci da na noma a rumbunan kayan abinci a jihohi da dama na Najeriya.

Sai dai a ranar Talata, ƙungiyar ta bayyana cewa an gano 48 da aka sace daga cikin 110.

Sace rufin gida da bahon wanka

Wata ɗabi'ar da masu satar suka ɓullo da ita, ita ce sace rufin kwano da kayan ɗaki da na kewaye musamman a gidaje ko ofisoshi ko kuma rumbunan ajiye abinci.

Hakan ya faru a Barnawa da ke Kaduna bayan da jama'a suka gama kwashe kaya, sai suka koma cire rufin ginin da ƙofofi.

Wasu jihohi kamar Legas ma irin hakan ta faru na ɓalle kofofi da tafiya da kayan kewaye.

Ko a ranar Talata sai da 'yan sandan Najeriya suka ce an kama fiye da mutum 800 da ake zargi da sace-sacen kayan abinci a rumbunan ajiye kayayyaki da ke jihohin ƙasar inda a jihar Legas kaɗai, an kama mutum 520.

Sace katifu a sansanin NYSC na Abuja

A ranar Talata ne wasu da ake zargin 'yan daba ne suka afka sansanin masu yi wa ƙasa hidima na NYSC da ke Kubwa inda suka saci katifu da babura da sauran kayayyaki a sansanin.

Mutanen sun isa wurin ne da safe inda suke tunanin akwai kayan abinci na tallafin gwamnati da aka ajiye a wurin

Sai dai tuni 'yan sanda da sojoji suka isa wurin inda suka fatattaki mutanen tare da killace wurin domin hana mutane ci gaba da wawushe abubuwan domin kai ɗauki da kuma killace wurin.

Satar magunguna a asibitin masu taɓin hankali

Ɗaya daga cikin manyan abin mamaki a jerin sace-sacen nan shi ne yadda wasu suka afka asibitin kula da masu taɓin hankali da ke birnin Calabar inda suka lalata magungunan da kuma buɗe wa marasa lafiya ƙofa su fita.

A wani bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta, an ga ɓarayin na tafiya da talabijin da firiji da janareto da dai sauransu.

An ga kuma waɗanda suka kai harin sun farfasa motocin asibitin tare da tafiya da gadajen da marasa lafiyan ke kwana.

An sace gilashin da ke jikin mutum-mutumin Awolowo

Bayan zanga-zangar #ENDSARS da aka yi a Legas, kwatsam sai aka lura cewa wannan gilashin da ke jikin mutum-mutumin Obafemi Awolowo ya yi ɓatan dabo.

Babu wani ƙarin bayani kan waɗanda suka yi wannan aika-aikar, amma ana ganin waɗanda suka lalata wurare yayin zanga-zangar ne suka yi hakan.