An fara binciken zargin cin zalin 'ƴan sanda da labari mai ɗaga hankali

Matasa ne yawanci suka mamaye zanga-zangar #EndSARS da ke zargin ƴan sanda da cin zalinsu
Bayanan hoto,

Matasa ne yawanci suka mamaye zanga-zangar #EndSARS da ke zargin ƴan sanda da cin zalinsu

Shaidu na farko kan binciken cin zalin ƴan sanda da aka fara a Najeriya ya bayyana yadda jami'an rundunar yaƙi da fashi da makami ta SARS da aka rusa suka azabtar da shi tare da cire harakoransa.

An kama Okoye Agu bayan maigidansa ya zarge da yin sata a wajen aiki.

An fara binciken cin zalin ƴan sanda ne a jihar Legas sakamakon zanga-zangar kiran a rusa rundunar SARS .

Kwamitin binciken zai diba harbin da ake zargin sojoji sun yi kan masu zanga-zanga a makon da ya gabata inda ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam suka ce an kashe mutum 12.

A lokacin da yake bayar da shaida, Mista Agu ya ce a 2014 an yi masa dukan tsiya tare da gabatar da shi a bainar jama'a a matsayin mai laifi, an dawo da kansa ƙasa haƙoransa biyu suka fita, sannan aka sayar da motarsa da wayarsa ta salula ba tare da izininsa ba.

Ƴan sanda sun ki biyansa duk da kotu ta bukaci su biya diyya, kamar yadda ya shaida wa kwamitin binciken da tsohon alƙali ke jagoranta.

Ya ce iyalinsa ba su san idan yake ba kuma lokacin da suka tafi ofishin ƴan sanda bayan kwana 47 suna nemansa, matarsa da mahaifiyarsa an yi masu duka a gabansa.

Abubuwan da Mista Agu ya gani sun yi daidai da sauran zarge-zarge da ake yi wa jami'an SARS, waɗanda ake zargi da ƙuntatawa wani lokaci har da kisa.

An ɗage sauran ƙararraki uku da aka shirya za a saurara a ranar Talata saboda wasu shaidun ba su halarci zaman ba.

Zargin da ake yi wa rundunar SARS da ƴan Najeriya suka ƙi jini ya haifar da zanga-zanga a sassan ƙasar, matakin da ya tilasta wa shugaba Muhammadu Buhari rusa rundunar.

Kaddamar da binciken na musamman kan yadda ƴan sanda ke cin zalin mutane ya kasance babbar buƙatar masu zanga-zangar.

Bayanan hoto,

An shafe mako biyu ana zanga-zangar EndSARS a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta buƙaci dukkanin jihohin ƙasar 36 suka kafa kwamitin bincike, kuma Legas ce ta farko da ta fara sauraren koken waɗanda suka gabatar da kansu kan zargin ƴan sanda da cin zarafinsu.

Kwamitin binciken na mutum 11, wanda ya ƙunshi mutum biyu daga ɓangaren masu zanga-zanga zai ci gaba da sauraren ƙorafi na tsawon wata shida.

  • Saurare da hujjoji da waɗanda jami'an SARS suka ci zarafi suka gabatar
  • Za su tantance ko ya dace a biya diyya
  • Za su tantance ko za a hukunta jami'an da ake zargi da cin zarafi
  • Bayar da shawarwari kan yadda za kaucewa cin zarafin mutane

Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya sanar da cewa binciken ya shafi har da al'amarin da ya faru a Lekki a ranar 20 ga Oktoba inda wasu daga cikin masu zanga-zanga da kuma kungiyoyi kamar Amnety Internetional suka ce sojoji sun buɗe wa masu zanga-zanga wuta, kuma wasu sun mutu.

Sai dai rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin jami'anta da bude wa masu zanga-zanga wuta

Wasu ƙarin labarai kan zanga-zangar #EndSARS:

Wakilin BBC ya ce mutane za su zura ido don ganin yadda gwamnati za ta aiwatar da shawarwarin kwamitin idan ya kammala bincikensa, kasancewar an daɗe hukumomi a Najeriya na yin biris da sakamakon binciken kwamitin da aka kafa don gudanar da bincike.

Misali, kamar shawarwarin da kwamitin binciken kisan ƴan shi'a mabiya Zakzaky da sojoji da ake zargin sojoji sun yi har yanzu hukumomi ba su aiwatar ba.