Waɗanne tambayoyi kuke da su kan duk abin da ya shafi zanga-zanga a tsarin ƙasa?

endsars protest london

Tun a farko-farkon watan Oktoban 2020 ne wasu ƴan Najeriya suka fara zanga-zangar nuna adawa da cin zarafin da sashen ƴan sanda mai yaƙi da fashi da makami a ƙasar ke yi wa jama'a.

Daga baya lamarin ya munana ta yadda ya rikiɗe ya zama rikici har ya jawo asarar rayuka.

Mutane da dama a ciki da wajen ƙasar sun goya wa masu zanga-zangar baya, yayin da wasu ke ganin an fara zanga-zangar ne don a hargitsa al'amuran gwamnati.

To mece ce ma zanga-zanga a bisa tsarin ƙasa?

Ku aiko da tambayoyinku kan abin da kuke so ku sani kan abin da ya shafi zanga-zanga a tsarin ƙasa, BBC kuma za ta gudanar da bincike tare da kawo muku cikakkiyar maƙala.

Ku sanya sunanku a ƙasa idan kuna son a wallafa tambayarku a cikin maƙalar.