Ƙayatattun hotunan Afrika na wannan makon: 16 - 22 October 2020

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotuna daga nahiyar Afrika:

Bayanan hoto,

An ɗauki wannan hoton ne a daidai lokacin da rana ke shirin fitowa a Tafkin Salt da ke Masar

Bayanan hoto,

Wata yarinya 'yar makaranta kenan sanye da takunkumi a Cairo babban birnin ƙasar

Bayanan hoto,

Wasu mata kenan da ke kan layi suna jira su jefa ƙuri'a a rumfar zaɓe lokacin zaɓen shugaban ƙasa a Guinea a ranar 18 ga watan Oktoban 2020.

Bayanan hoto,

Kwana ɗaya bayan zaɓen Guinea, wani mai goyon bayan jam'iyya mai mulki kenan a Ivory Coast inda yake sanye da hula da aka rubuta taken jam'iyyar. Za dai a yi zaɓen shugaban ƙasar a ƙarshen watan nan.

Bayanan hoto,

Wata mata kenan a ranar Alhamis ke wucewa ta gaban wani zane da ke tuna wa mutane su rinƙa saka takunkumi a birnin Abidjan na Ivory Coast

Bayanan hoto,

Wasu magoya bayan wasan ƙwallon ƙafa kenan ke shewa da nuna jin daɗi yayin wata gasar ƙwallon ƙafa a Aljeriya a ranar Juma'a

Bayanan hoto,

Wani ɗan Najeriya kenan mazaunin Afrika Ta Kudu a ranar Laraba yayin da ya yi wani aski da ke alamta taken ENDSARS, ma'ana kawo ƙarshen rundunar da ke yaƙi da fashi da makami a Najeriya

Bayanan hoto,

Waɗannan masu zanga-zangar na jihar Ogun na daga cikin dubban mutanen da suke zanga-zanga a Najeriya kan rundunar ENDSARS.

Bayanan hoto,

An ɗauki wannan hoton ne a ranar Alhamis bayan wasu da ake zargin jami'an tsaro ne sun buɗe wuta ga masu zanga-zangar ENDSARS a Legas

Duka waɗannan hotunan na da haƙƙin mallaka, kuma mun same su ne daga Reuters da EPA da kuma AFP.