Hotunan yadda hadarin tsuntsaye ya ja hankalin mazauna wani yanki a Ingila

  • Daga Martin Barber
  • BBC News Online
Bayanan hoto,

''Da a ce duk kalmar mamaki ta 'kai' da 'wayyo Allahna' da na ji tsawon shekaru kan wasu ayyukana kuɗi ne, da yanzu na zama hamshaƙin mai kuɗi, in ji mai ɗaukar hoto Les Bunyan

Yawan tsuntsaye da suka tashi sama a lokaci guda suka samar da wani ''hadari'' a sararin samaniya a yankin Norfolk da ke gaɓar teku ya kai wani adadi da ba a taɓa samun irinsa ba.

A karon farko an ga kusan tsuntsaye 140,000 a wani gandun dabbobi na ƙungiyar RSPB da ke Snettisham. Yawan tsuntsaye na baya da aka taɓa gani shi ne 120,000 a lokacin hunturu tsakanin shekarun 1990 zuwa 1991, a cewar ƙungiyar.

Kallonsu kaɗai ya zama wani ''yanayi mara misaltuwa'', a cewar mai ɗaukar hoto Les Bunyan, wanda ya yi aikin sa kai a gandun da ke gaɓar teku na Wash.

''Ba wai kallonsu ne kawai abin sha'awa ba, kukan tsuntsayen ma abin ɗaukar hankali ne. Idan dubun-dubatar tsuntsaye na zagaye a kewayen da kake - to za ka ji suna ta fitar da sauti daban-daban.''

Bayanan hoto,

"Ina jerin hotunan da na ɗauka na irin wannan hadarin tsuntsayen a sarrain samanyi a yayin da launinta ya zama ruwan goro alamar faɗuwar rana''

Tsuntsayen, waɗanda tsayinsu ya kai kusan inci 10, sun yi ƙaura mafi tsawo da kowace irin dabba ta taɓa yi daga yankin Arctic da suke rayuwa zuwa gaɓar tekuna a nahiyar Turai da Afirka da Australiya inda suke zama a can a lokacin hunturu don samun abincinsu.

Mr Bunyan mai shekara 64, ya shafe shekara 20 yana ɗaukar hotunan namun daji, ya kuma ce ɗaukar hadarin tsuntsayen wani abu ne da ya zame masa jiki.

"Ina ga abin da ya fi jan hankali idan tsuntsaye suka tashi sama - shi ne yadda nake ji na na dawo ɗan ƙarami,'' a cewarsa.

''Ina ga ya kamata kowa ya dinga mayar da hankali kan irin waɗannan abubuwan - ku gwada fita wajen don kallon irin hakan ku ga yadda za ku ji.''

Bayanan hoto,

Idan tsuntsayen suka taru jingim sai su tashi sama su yi tamkar hadari su kuma bayar da wata da'ira mai kyau

A lokacin da aka sanya dokar kulle don kare yaɗuwar annobar cutar korona a watan Maris, lokacin da Mr Bunyan ya samu shafe lokaci sosai a gaɓar tekun Wash ya taka muhimmiyar rawa a wajensa.

''Fita waje na da matuƙar amfani a gare ku da ma lafiyar ƙwaƙwalwarku. Ni dai hakan ya taimake ni.''

Bayanan hoto,

"Na ɗauki jerin hotuna a yayin da tsuntsayen suka tashi sama suka yi tamkar gajimare musamman da yake launinsu baƙi da fari ne don ku ga wani abu mai ban sha'awa.''

Bayanan hoto,

"Ina ga abu ne mai matuƙar muhimmanci sosai saboda wataƙila a nan ne kawai za ku iya ganin waɗannan tsuntsayen akai-akai a ƙasar nan''

Bayanan hoto,

Taron tsuntsaye a sama ko a ƙasa duk abin sha'awa ne - Kallonsu da jin sautin kukansu duk abin daɗi ne. Duk wanda ya taɓa gani ba zai taɓa manta yadda abin yake ba''