Yadda tufafi ke sanya 'yan ƙabilar Oromo a Ethiopia na alfahari da kansu

  • Daga Elias Hordofa
  • BBC Afaan Oromoo

Duk da cewa 'yan kabilar Oromo na kasar Ethiopia su ne suka fi rinjaye a kasar, amma sai a baya bayan nan ne suka rika fitowa fili su bayyana asalin al'adu da kabilarsu.

Hakan ya kai ga kaucewa yin magana da harshensu, Afaan Oromo, a bainar jama'a don fargabar kada a rika sukarsu kan rashin bin ka'idar nuna asalin 'yan kasa.

Amma kuma karuwar jajircewa kan ra'ayin siyasa, hada da yin alfahari da al'adun a tsakanin matasa 'yan kabilar ta Oromo a shekaru goma da suka gabata ne suk sa suke nuna hakan ta hanyar adon tufafi.

Ana kallon bikin Ireecha na nuna godiya ga Allah, wanda 'yan kabilar Oromo ke gudanarwa a duk shekara a matsayin wata dama ta yin nuni da sabbin tufafi.

A wani bangaren, telolin zamani kamar su Antiko Designs, suna zamanantar da irin dinkunan da suke yi.

Ja, baki da fari su ne ba tare da wata-wata ba ake ganewa a matsayin launukan Oromo, kuma a yayin da mazan da ke cikin hoton sama suka yi shigar jamfa da wando na gargajiya har da dankwali, su kuwa dogayen rigunan matan wani sauyi ne na saka tufafin gargajiya.

Su kuwa dogayen sandunan da ake kira siinqee, wani salon al'adunsu ne da ke taimakawa wajen kare martabar mata a cikin al'umma.

A wadannan tufafi wadanda shagon dinki na 'Kush Design' ya dinka, kana iya ganin irin ado da launukan 'yan kabilar Oromo da aka jera a zagayen jikin da kuma hannayen.

Elias Badhaasaa, mai daukar hoto, ya matsu ya dauki wadannan hotuna don kara fito da al'adunsu.

Ya shaida wa BBC cewa: "Nakan ga ana ta daukar hotunan kayan al'adun gargajiya na wasu kabilun tare da adana su amma banda namu''.

"Saboda haka, ni ma na fara tambayar kaina, me ya sa mu ba ma son tallata namu al'adun? Ina son a san da ni a ciki da wajen kasashen gabashin Afirka.''

Yankin Oromia yana da fadin gaske a kasar Ethiopia kuma yana da al'adu daban-daban.

A hoton da ke sama, mata ne daga gabashin Oromia dauke da kwanduna, amma baya ga damarar da ke suke daure da ita, shagon dinkin tufafin gargajiya na Yoomiyyu da ke kudancin yankin ne suka dinka.

Miliyoyin mutane ne kan halarci wannan biki na Irreecha a duk shekara, amma a wannnan shekarar saboda dokokin cutar korona an takaita yawan mutanen a Addis Ababa babban birnin kasar.

Wannan shi ne karo na biyu kawai da ake gudanar da bikin a birnin, da ke nuna girman tagomashinsa a kasar.

Matar da ke rike da sandar siinqee a wannan hoto na sanye da cikakken tufafin gargajiya na 'yan kabilar Oromo, amma kuma akwai wasu ado irin sa a jikin tufafin matar da ke kusa da ita da suka fi sabunta.

Wani abin daukar hankali shi ne karin tsarkakkiyar bishiyar Odaa wacce ita ce alamar bajon kabilar Oromo.

Shekaru hudu da suka gabata, wani abin bakin ciki ya faru a taron bikin, lokacin da mutane akalla 55 suka rasa rayukansu a wani turmutsutsu wanda wata arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga ta haddasa. Amma kungiyoyi masu rajin kare hakkin bil adama sun ce wadnda suka rasa rayukan nasu sun kai daruruwa.

Wadannan wasu jerin zanga-zanga ne da 'yan kabilar Oromo suke gudanar, da suka jima suna kokawa kan yadda nuna wariya a bangaren siyasa da tattalin arziki ke karuwa.

Tun bayan wannan lokaci ne aka samu sauyi a bangaren siyasa a kasar, bayan da Firaiminista Abiy Ahmed ya karbi ragamar Mulki- wanda shi ma dan kabilar Oromo ne - amma an dan ci gaba da samun damuwa.

Gangamin neman 'yancin Oromo ya samu goyon bayan 'yan kasar mazauna kasashen waje, musamman a Amurka.

Batun da ya ja hankulan jama'a na rungumar saka tufafin gargajiya ya kai har can, ta yadda za ka iya ganin hotuna daga 'RedFox Apparel', wanda aka dauka a jihar Minnesota.

Wata matashiya mai zayyana tufafi Senakebeki Girma, mai kimanin shekaru 27, ta bayyana sauya tunani kan yanayin adon tufafin 'yan kabilar Oromo a matsayin "abin ban mamaki'' tana mai bayyana cewa "mutane na kara yin alfahari da al'adun kasarsu''.

Yanzu tana bukatar ta ga tufafin kabilar ta Oromo a koda wane lokaci ba sai a lokacin irin wadannan bukukuwa ba.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.