SecureNorth: Ali Nuhu ya gamu da fushin 'yan Twitter kan rashin tsaro a Arewa

.

Fitaccen tauraron fina-finan Kannywood, Ali Nuhu, ya yi amai ya lashe sakamakon a yanzu ya shiga zanga-zangar #SecureNorth, inda a baya ya ƙi shiga zanga-zangar kan wasu dalilai nasa.

A baya dai, dalilin da ɗan wasan ya bayar na ƙin shiga gangamin da aka shirya na jawo hankalin mahukuntan Najeriya kan rashin tsaron da arewacin kasar ke fama da shi ya janyo masa matukar suka a shafin Twitter amma duk da haka, tauraron ya shaida wa BBC cewa shi ko a jikinsa.

Tun a farkon mako ne wasu al'ummar arewacin kasar suka soma gangami domin yin tur da irin halin tabarbarewar tsaro da yankin ke ciki.

Sai dai da alama a yanzu jarumin ya bi sahun masu zanga-zangar inda ya wallafa wani saƙo a shafinsa na Instagram na goyon bayansu.

Sun kirkiri maudu'i mai taken #SecureNorth, wato a kawo tsaro a Arewa, domin jan hankalin gwamnatin Shugaba Muhamadu Buhari kan irin ta'asar da 'yan bindiga da masu satar mutane da ma mayakan Boko Haram suke ci gaba da yi.

Hakan na zuwa ne a yayin da 'yan Najeriya, musamman daga kudancin kasar, ke ci gaba da zanga-zangar kyamar kashe-kashe da azabtarwar da ake zargin rundunar SARS take yi, abin da ya sa gwamnati ta rusa ta.

Masu zanga-zanga kan rashin tsaro a arewacin kasar sun bayyana wa manema labarai cewa yankin ne ya fi cancantar samun kulawar gaggawar gwamnatin Shugaba Buhari ganin cewa ya dade yana fama da matsalolin rashin tsaro, abin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane, kana ya raba dubbai da gidajensu.

Bayanan hoto,

Ali Nuhu ya ce ba ya yin abu don "burge mutane"

Me Ali Nuhu ya ce?

Sai dai a hirarsa da gidan rediyon DW Hausa, Ali Nuhu ya ce wasu daga cikin taurarin fina-finai suna tsoron shiga irin wadannan gangami ne saboda ba sa so a rika zaginsu.

"Wani lokacin, kai a matsayinka na tauraro in za ka shiga wata maganar, sai ka ga kamar shisshigi za ka yi wa mutane," in ji shi.

"Ka je Twitter, a nan ne za ka ga an saka taurarin Arewa a gaba ana zaginsu, a kushe su, a yi musu wulakanci yadda rai yake so. Wannan shi ne dalilin da ya sa mutane suke ja baya-baya ba wai ba sa son shigowa ba ne."

Martani

Sai dai da alama wadannan kalamai sun yi matukar bata ran masu amfani da shafin Twitter na Najeriya, inda suka yi ta yi masa raddi.

Hasalima, sunan Ali Nuhu na cikin manyan batutuwan da aka fi tattaunawa a shafin na Twitter tun daga daren Asabar zuwa yau Lahadi, inda mutum fiye da 19,000 suka yi tsokaci a kansa.

Bayanan hoto,

Ali Nuhu ya ce tsoron cin mutunci ne yake hana wasunsu shiga fafutuka

Wani mai suna Safiyanu a Twitter yana ganin cewa Ali Nuhu bai damu da rayuwar masu kallonsa ba tun da ba ya son ya shiga gwagwarmaya saboda ba ya so a soke shi.

Shi kuwa Alamin kira ya yi ga 'yan Arewa "mu farka don muna da buri wanda shi ne tabbatar da tsaro a Arewa sannan mu kawar da rashin tsaro. Ku manta da Ali Nuhu. Allah na tare da mu.'

Amma a nasa bangaren, Zannah, ya yi kira ga masu fafutukar tabbatar da tsaro a Arewacin Najeriya su mayar da hankali kan fafutukar domin cimma burinsu maimakon sukar Ali Nuhu.

Da yake yin raddi kan masu sukarsa a Twitter, tauraron ya shaida wa BBC cewa ko a jikinsa.

"Ba na yin abu don in burge mutane," in ji Ali Nuhu.

Ya ce yana tausaya wa masu wannan fafutuka domin shi yana yin abin da yake ganin ya dace ne.

"Ku je shafina na Instagram ku ga abin da na yi," a cewarsa, inda yake magana kan irin kudaden da ya bai wa wasu mabiyansa domin su ja jari.

Ba a taru an zama daya ba

Sai dai a yayin da Ali Nuhu ya ce wasu daga cikinsu ba sa son shiga irin wannan fafutuka saboda tsoron zagi, wasu fitattu a Kannywood, irin su Ali Jita, sun rungumi fafutukar inda suke kira kowa ya sa hannu wajen ganin an tabbatar da tsaro a Arewa.

"Wasu daga cikin abubuwan da zanga-zangar #SecureNorth ta rasa su ne rashin tsari, da goyon baya daga wurin lauyoyi da masu fafutuka da masu hada ta.

"Muna bukatar lauyoyi da masu fafutuka da 'yan jarida su ba mu goyon baya. Hakan zai rage barazanar da muke fuskanta daga 'yan sanda da ke karbar kudi a wurin mutane," in ji shi.

Da alama kiran nasa ya fada kunnen manya, domin kuwa mai ɗakin Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta bi sahun masu kira a kawo ƙarshen rashin tsaron da ke addabar Arewacin Najeriya.

Matar shugaban kasar ta wallafa wani saƙo a shafinta na Twitter ranar Asabar tare da wakar mawakin Kannywood Adam A. Zango, inda yake kokawa kan matsalar tsaro da ta addabi arewacin Najeriya.

Sakon nata na ɗauke da maudu'in #Achechijamaa, wanda ke nufin a ceci rayuwar jama'a.

Wakar na ɗauke da hotunan Shugaba Muhammadu Buhari tare da manyan hafsoshin tsaron kasar yayin da suke ganawa a fadar shugaban ƙasa.