Ƙayatattun hotunan wasu abubuwan da suka faru a Afirka a makon nan: 9-15 ga Oktoban 2020

Ga wasu zaɓaɓɓun hotunan wasu abubuwan da suka faru a Afirka a makon nan:

Bayanan hoto,

A ranar Litinin dalibai sun karbi shaidar kammala digiri insu a babban birnin Guinea, Conakry...

Bayanan hoto,

...An liƙa fastocin ƴan takara a ko ina a cikin gari domin tuna wa mutane zaɓen shugaban kasa ranar Lahadi inda Alpha Condé zai sake tsayawa takara a karo na uku...

Bayanan hoto,

...Cellou Dalein Diallo zai fafata da Mr Condé, magoya bayansa kamar wannan mutumin, na ɗauke da zanen ɗan takarar tasa sauran magoya baya kuma na buga gangar goyon baya.

Bayanan hoto,

A ranar Litinin wata mai zanga-zanga a Legas ta tsaya a kan mota tana neman a yi wani abu game da zaluncin ƴan sanda a Najeriya...

Bayanan hoto,

... kwana ɗaya bayan nan wani mai zanga-zangar a Abuja, babban birnin Najeriyar, shi kuma ya fito da nasa salon don jan hankalin jama'a.

Bayanan hoto,

A ranar Laraba a Mogadishu na Somaliya, wani mutum na jiran babur mai ƙafa uku su wuce kafin ya tsallaka titi.

Bayanan hoto,

A ranar Laraba, wasu masu aikin sa kai a birnin Johannesburg na Afirka Ta Kudu, suna miƙa taimakon abinci ga mutanen da ke cikin yanayin kullen cutar korona.

Bayanan hoto,

A ranar Litinin yara a Kenya sun koma makarantu tun bayan rufe su da aka yi a Maris domin rage yaduwar Korona.

Bayanan hoto,

A wani wuri a Afirka Ta Kudu a wannan ranar dai, mutane sun haɗa hannu domin yin addu'a a garin Senekal, inda can ne cibiyar tashin hankali kan hare-haren da ake kai wa Turawa manoma.

Bayanan hoto,

A ranar Litinin gwamnatin Libiya da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yarda da ita ta sanya nakiyar da aka gano a kusa da Tripoli babban birnin ƙasar.

Dukkan hotunan suna da hakkin mallaka.