Sanjay Dutt ya ce ya kamu da cutar kansa

Sanjay Dutt file photo
Bayanan hoto,

Dutta ya yi fice sosai a fina-finan Indiya

Fitaccen tauraron fina-finan Indiya Sanjay Dutt ya tabbatar da cewa ya kamu da cutar kansa bayan da aka shafe makonni ana yaɗa jita-jitar hakan a kafafen yaɗa labaran ƙasar.

A wani saƙon bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, jarumin mai shekara 61 wanda ya yi fina-finai fiye da 150, ya ce ''nan ba da daɗewa ba zai shawo kan cutar sannan zai fara ɗaukar sabon fim ɗinsa a watan Nuwamba.

A watan Agusta Mista Dutt ya kamu da cutar korona bayan da ya fara samun matsalar shaƙar numfashi. An yi gwaji an kuma gano ya kamu da cutar.

Daga baya aka gano yana ɗauke da wasu cututtukan daban a asibitin Mumbai Lilavati.

A watan Agusta Mista Dutt ya ce ''ya ɗauki gajeren hutu daga aiki don kula da lafiyarsa'' a lokacin da ake ta yaɗa rahotannin da ba a tabbatar ba da ke cewa ya kamu da cutar kansar huhu.

Jarumin da matarsa Maanayata sun fitar da sanarwa daban-daban, suna masu ƙarfafa wa magoya bayansa gwiwar cewa kar su damu da jita-jitar da ake yaɗawa kan lafiyarsa.

A wani bidiyonsa na baya-bayan nan da ya yi a shagon askin da ya ke zuwa, Dutt ya ce: ''Wannan ne tabo na baya-bayan nan da na samu a rayuwata. Amma zan magance shi. Kwanan nan zan warke daga cutar kansa,'' a cewarsa.

Ya ƙara da cewa yana ''farin cikin sake komawa fagen ɗaukar fim'' a fim ɗinsa na gaba.

Ya yi fice sosai a fagen fim na Indiya, amma ya ɗan dakatar da yin fina-finai sakamakon komawarsa gidan yari a 2013 don kammala shekara biyar ɗinsa.

An kama shi ne da laifukan mallakar makamai da ke da alaƙa da hare-haren da aka kai Mumbai a 1993 da ya yi sanadin kashe mutum 257 sannan mutum 713 suka jikkata.

A 2016 ya sake komawa fagen sana'arsa.

Mutum biyu a danganinsa sun mutu sakamakon cutar kansa. Mahaifiyarsa Nargis ta mutu sakamakon kansar hanji a 1981, sannan matarsa ta fari ma kansar ƙwaƙwalwa ce ta kashe ta.