Adadin waɗanda suka kamu da cutar korona a Najeriya ranar Talata ya kai 168

Wasu ma'aikatan lafiya a Najeriya
Bayanan hoto,

Wasu ma'aikatan lafiya a Najeriya

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 168 da suka kamu da cutar korona a ranar Talata a ƙasar.

Da wannan sabbin alƙaluman jimillar wadanda cutar ta kama a ƙasar sun kai 66,607, ko da yake an sallami mutum 62,311.

Adadin waɗanda suka kamu da cutar a ranar Talata ya fi yawa a Abuja, inda aka samu mutum 61, sai Legas mai mutum 50 da Kaduna da aka samu mutum 27.

Sauran jihohin sun haɗar da Oyo mai mutum 12, da Rivers mai mutum 6, sai Katsina mai mutum 5, da Ogun mai mutum 3, da Kwara mai mutum 2, sai kuma jihar jihar Kano da aka samu mutum ɗaya kacal.

Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar coronavirus

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar numfashi ta coronavirus.

Yaya zan kare kaina daga cutar?

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:

■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.

Bayanan bidiyo,

Yadda mutane ke rayuwa cikin kullen korona a wani gidan gajeyu a legas