Kasuwar ‘Yan wasa: Calhanoglu, Alaba, Son, Lundstram, Gravenberch, Mustafi, Pochettino

Calhanoglu

Manchester United na tunanin dauko dan wasan tsakiya na AC Milan Turkiyya Hakan Calhanoglu, mai shekara 26. (Gazetta dello Sport - in Italian).

Calhanoglu a watan gobe ne zai tattauna makomarsa a Milan. (Mail).

Dan wasan da Liverpool ta ke nema David Alaba akwai yiyuwar zai tafi bayan kasa kulla yarjejeniya da Bayern Munich. Dan wasan na Austria mai shekara, 28, tun watan Janairu kwangilarsa da Bayern ta kawo karshe. (Bild via Daily Star).

Tottenham's na fatan sabunta kwangilar dan wasan na gaba Son Heung-min, mai shekara 28, bayan dan wasan na Koriya Ta Arewa ya shiga kamfani daya da Jose Mourinho. (TalkSport).

Amma, Mourinho ya ce ba zai tursasawa dan wasan ba. (Star).

Dan wasan tsakiya na Ingila John Lundstram zai bar Sheffield United bayan kasa cimma yarjejeniya da kulub din. Dan wasan mai shekara 26 ana alakanta shi da Burnley da Crystal Palace. (Sky Sports).

Barcelona ta kara samun kwarin guiwar ajiye Messi mai shekara Lionel Messi, 33, bayan shugaban kulub din Josep Maria Bartomeu ya yi murabus. (Telegraph).

Manchester United ta shiga hamayya da Barcelona da Juventus kan dan wasan Ajax mai shekara Ryan Gravenberch. (Mirror).

Tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino na tattauna da Zenit St Petersburg domin zama sabon kocinta. (Championat, via Sun).

Dan wasan baya na Arsenal da Jamus Shkodran Mustafi ya ce bai tattauna batun sabunta kwangilar shi da kulub din ba. Kwangilar dan wasan mai shekara 28 za ta kawo karshe ne idan an kammala kaka. (Evening Standard).

Mustafi na son ci gaba da taka leda a Emirates duk da rahotannin da ke cewa ya yi watsi da tayin sabuwar yarjejeniya. (Express).

Arsenal na son bayar da aron Reiss Nelson wannan kakar amma dan wasan na son kwatar wa kansa wuri a tawagar Mikel Arteta. (Independent).

Tsohon dan wasan Arsenal da West Ham Jack Wilshere, mai shekara 28, ya ce yana sauya sheka daga Premier League inda ya nuna son koma wa gasar Major League Soccer . (Sky Sports).

Atletico Madrid na neman wanda zai maye gurbin dan wasan Ghana Thomas Partey, mai shekara 27, bayan komawarsa Arsenal.

Atletico na neman dan wasan Valencia da Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya Geoffrey Kondogbia, mai shekara 27. . (Mundo Deportivo - in Spanish)

Tsohon kocin Arsenal manager Arsene Wenger yana ganin sabon Lig din Turai na manyan kungiyoyi Super League zai lallata Premier League. (Guardian)